IDAN MUTUM YANA SO YA CANZA SUNAN SHI, YA ZAI YI?
https://chat.whatsapp.com/JLojawdOWYsEOeSHZMNdjf
*TAMBAYA*❓
Assalamu Alaikum. Allah ya karawa rayuwa malam albarka tare da dukkan iyalinka. Don Allah Malam idan za'a canza ma mutum suna wacce hanya za'abi
*AMSA*👇
Wa alaikumus salamu wa rahmatullahi wa barakatuh. Alhamdu lillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu ala rasulillahi wa ala alihi wa sahbihi ajma'in.
Kawai zaka ambaci sunan da ka canza ga mai sunan ne. Domin Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya canza wa sahabbai sunaye mazan su da mata, ba tare da yanka ko wani dogon zance ba. Kawai idan Annabi ya ji sunan ka bai dace ba, sai yace kawai sunan ka wane, shike nan misali, wata tace sunan ta Asiyah, sai yace, a'a, sunan ki Jamila
«4954» حدثنا أحمد بن حنبل ومسدد قالا: حدثنا يحيى عن عبيد الله عن نافع عن ابن عمر أن رسول الله صلى الله عليه وسلم غير اسم عاصية وقال: ((أنت جميلة)).
Ya kuma ji sunan shi Asram, sai yace a'a, sunan ka Zur'ah
عَنْ عَمِّهِ أُسَامَةَ بْنِ أَخْدَرِيٍّ أَنَّ رَجُلاً يُقَالُ لَهُ أَصْرَمُ كَانَ فِي النَّفَرِ الَّذِينَ أَتَوْا رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَقَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: ((مَا اسْمُكَ)). قَالَ أَنَا أَصْرَمُ. قَالَ: ((بَلْ أَنْتَ زُرْعَةُ)).
Wani ma yace sunan sa Abul Hakam sai Annabi yace, Allah shine Alhakam. Ya tambaye shi ko kana da yaya, sai yace eh. Sai yace wanene babban su, sai yace Shuraih, sai yace, toh a kira ka Abu Shuraih
عَنْ أَبِيهِ هَانِئٍ أَنَّهُ لَمَّا وَفَدَ إِلَى رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ مَعَ قَوْمِهِ سَمِعَهُمْ يَكْنُونَهُ بِأَبِي الْحَكَمِ فَدَعَاهُ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَقَالَ: ((إِنَّ اللَّهَ هُوَ الْحَكَمُ وَإِلَيْهِ الْحُكْمُ فَلِمَ تُكْنَى أَبَا الْحَكَمِ)).
Haka ya ji an kira wani da sunan Haznun, sai yace a'a, sunan ka Sahlu
عَنْ أَبِيهِ عَنْ جَدِّهِ أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ لَهُ: ((مَا اسْمُكَ)). قَالَ حَزْنٌ. قَالَ: ((أَنْتَ سَهْلٌ)).
قَالَ لاَ السَّهْلُ يُوطَأُ وَيُمْتَهَنُ. قَالَ سَعِيدٌ فَظَنَنْتُ أَنَّهُ سَيُصِيبُنَا بَعْدَهُ حُزُونَةٌ.
Wallahu ta'ala a'lam
*_Amsawa_* :
*Malam Aliyu Abubakar Masanawa*
Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
*_Group Admin: ▽_*
*MAL. HAMISU IBN YUSUF*