ILIMI SHI NE KOMAI

ILMI SHINE KOMAI. 

Al-Imam Ibnul Jauzi Allah ya masa rahama yana cewa "Duk Wanda yake so ya zama magajin Annabawa, kuma Mai girbi a gonansu to ya nemi ilmi Mai amfani, wanda shine ilmin addini, kamar yadda yazo a hadisi "Malamai magada Annabawa ne". Yana halartar wuraren karatu domin wurin karatu dausayi ne daga cikin dausayin Aljannah. Duk Wanda yake so ya samu kulawar Allah agareshi to ya waiwaya ya duba matsayinsa wurin fahimtar addinin Allah, domin yazo ahadisi "Duk wanda Allah yake son sa da alkhairi zai fahimtar dashi Addini. Duk wanda yake neman hanyar da zata kaishi zuwa Aljannah to ya tafi zuwa majalis na ilmi, domin yazo a hadisi "Duk wanda ya kama hanyar neman ilmi to Allah zai saukake masa hanyar samun aljannah". Duk wanda kuma yake son kada ladansa ya yanke bayan mutuwarsa to ya yada ilmi ta hanyar rubuce rubuce da kuma karantarwa, domin yazo a hadisi "Idan mutum ya mutu ayyukansa duk sun tsaya sai guda uku, sadaqa Mai gudana, ko wani ilmi da ya bari ake amfanuwa dashi, ko wani yaronsa na gari da zaina masa addu'a".

التذكرة في الوعظ ١/٥٥ 

#Zaurenfisabilillah 

https://t.me/Fisabilillaaah

Post a Comment (0)