INA YA KAMATA NA KALLA A JIKIN BUDURWA TA?


*INA YA KAMATA NA KALLA A JIKIN BUDURWATA ?*

*Tambaya:*

Assalamu alaikum,
Malam ko ya halatta in kalli gashin macen da nike so in aura? Ko kuma don Allah malam ka taimaka kaman bayanin abunda ya halatta in kalla a jikin macen da zan aura kafin muyi aure. Na gode. Allah ya gafarta maka.

*Amsa:*
Wa'alaykumussalam,

To dan'uwa ya halatta ka kalli macen da kake so ka aura, kamar yadda ya zo a cikin hadisi, inda Annabi s.a.w. yake cewa : "Idan dayanku yana neman aure, to in ya sami damar kallon abin da zai kira shi zuwa aurenta, to ya aikata hakan" Abu dawud a hadisi mai lamba ta : 2082.

Malamai sun yi sabani akan wurin da ya kamata mutum ya kalla a jikin mace lokacin da ya je neman aure :

1. Akwai wadanda suka ce zai kalli fuska da tafin hannu ne kawai, saboda tafin hannu yana nuna ni'imar jikin mace, kamar yadda fuska take nuna kyau, don haka sai a takaita akan su, wannan ita ce maganar mafi yawan malamai.

2. Zai kalli duk abin yake bayyana a jikin mace, don haka bayan fuska da hannu zai iya kallon duga-dugai da wuya.

3. Wasu malaman sun tafi akan cewa : zai kalleta a kayan da take sawa a cikin gida, ta fuskace shi ya kalle ta, sannan ta juya baya ya kalleta.

Wannan ra'ayin shi ne ya fi dacewa, saboda ta haka mutum zai san yanayin matar da zai aura, yadda ya kamata.

Saidai ba'a son yawaita kallon saboda duk abin da aka halatta saboda bukata, to ya wajaba a tsaya a gwargwadonta, wannan yasa yawaita zuwa zance da yawaita yin waya, zai iya zama haramun saboda yana iya tayar da sha'awa, sha'awa tana iya kaiwa zuwa barna.

Allah ne mafi sani

Don neman Karin bayani, duba : Al'insaf 8\15 da Muhallah 9\161.

*Amsawa*✍🏻

*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*
12/04/2013
Post a Comment (0)