TASKAR TARIHI 28



*TASKAR TARIHI [28]*

 ```📌 GININ KA’ABAH``` 
 
*Al-Imamu Ibnu Hajar* yace: (ita Ka’abah ta kasance a Jahiliyya an ginata ne da Dutse, ba tareda an sanya Siminti ma na gini a tsakani ba, tsawon ta ya kasance gwargwadon yadda daga tsaye Wuya na ÆŠan’adam zai iya leÆ™ata, sannan Tufafin da ake lulluÉ“e Ka’abar sun kasance ana sawa ne akan Ka’abah a lulluÉ“a daga sama sai a rufeta, tanada kwanoni guda biyu, kamar yadda wannan zane yake na harafin Turanci, wato D. 

✂️ Ita Ka’abah ta kasance a kewaye take da gidajen mutanen Makkah, a cikin Saheehul Bukhaariy daga Amru Ibn Dinar da Ubaidullahi bn Abu Yazid sukace: (Babu wata Katanga da ta kewaye Ka’abah a zamanin Annabi SAW, don haka Sahabbai suna Sallah ne kewaye da Ka’abah, har zamanin Umar (RA) sai ya gina wata Katanga wadda ta kewaye Ka’abah din, Ubaidullahi yace: Katangu na wannan garu É—in gajeru ne, Ibnuz Zubair da yazo sai ya gina wannan Katanga a matsayin Masallaci). 
Don haka sai ita Ka’abah ta zama tana fuskantar barazana na kwararowar Ruwa, ruwan da yake kwararo mata daga duwatsun Makkah, saboda rashin samun wasu danni wanda zasu kare ta. 

✂️ Yayin da Manzon Allah SAW Ya kai Shekara Talatin da Biyar (35), sai wani ruwa mai yawa yazo, sai ya tsaga wannan Bango na Ka’abah, ruwan ya raunata tushen ginin, sai Ƙuraishawa sukayi nufin su rushe Ka’abah domin su gyarata, sai dai suka firgita suka ga kwarjinin haka, saboda matsayin Ka’abah a zuciyar su, da kuma tsoron da suka ji kada wani abu ya same su. 
Walidu yace: shin kuna nufin kyakkyawar manufa ne da rusa ita Ka’abar nan, ko kuwa mugun abu? Sai sukace: kai ma ka sani, kyakkyawar manufa ce tasa zamu rusa, sai yace: *Allah baya hallaka mutanen kirki,* sai ya É—auki Gatari, ya fara rusa Ka’abah, a wannan dare mutane suka kwana suna saurare su gani ko wani mugun abu zai samu Walidu, sai sukace: mu saurara, in wani abu ya same shi bazamu rusa komai ba, sai mu mai da ita kamar yadda take mu Tuba, idan kuwa wani abu bai same shi ba to zamu cigaba da rusata, Allah ya yarda da abunda muka aikata kenan.
 
✂️ Walidu kawai sai gashi ya wayi gari lafiya lau ba abunda ya same shi, sai ya koma wajen aikin shi na rusa Ka’abah, yaje ya cigaba da rusawa, sai suma sauran mutanen kuma suka taya shi, har saida suka isa zuwa ga inda Annabi Ibrahim (AS) yasa harsashin gini, suka kai zuwa ga wasu korayen duwatsu, sai akaga a wannan harsashi na Annabi Ibrahim ya manna sashin su da sashi don ya zama sun riÆ™e juna, wato yayi tsari irin na gini, don haka sai suka bar wannan harsashi kamar yadda yake, sai suka fara gini, sai suka hadu a tsakanin su kan cewa; kada su shigar da wasu KuÉ—i wajen wannan gini nata, na daga ayyukan da suke na neman KuÉ—i sai abunda yake na Halal ne, Kudin da Karuwa take samowa wajen Karuwanci bazai shiga wurin ginin Ka’abah ba, hakanan duk wanda yake Kasuwanci da Riba, ko kuma wata Cuta da akayi wa wani cikin Mutane. 

✂️ To sai Kuraishawa suka raba aikin ginin Ka’abah, don haka kowani tattaruwa na daga Ƙabilu sai suka riÆ™e wani É“angare wanda su suke ginawa, Manzon Allah ma Yayi tarayya wajen wannan ginin Ka’abah É—in, daga Jabiru bn Abdullah RA yace: _(yayin da aka gina Ka’abah sai Annabi SAW da Abbas RA sai suka tafi suna É—aukar dutsen da ake ginin Ka’abah, sai Abbas yace wa Annabi SAW: ka sanya gyautan ka dake É—aure a kwankwason ka, ka cire shi kayi gammo ka sashi a daidai wuyan ka, don ya hanaka daga shan zafin dutse É—in, Annabi yana cire wannan gyauto sai ya faÉ—i Æ™asa, idanuwan shi suka kakkafe a sama, sannan sai ya farfaÉ—o, sai akaji Annabi SAW Yana cewa: bani gyauto na, bani gyauto na, sai aka É—aura mishi gyauton shi, shikenan sai ya tashi._

✂️ Da Ƙuraishawa suka kai daidai inda ake É—aura Al-Hajarul Aswad sai saÉ“ani yazo musu cewa wanene zai É—aura shi?, kowace Ƙabila tana son ta samu wannan darajar, har saida YaÆ™i ya kusa faruwa a tsakanin su, Banu Abdud-Dar suka kawo wani Daro na cike da jini, suka Æ™ulla yarjejeniyar mutuwa tsakanin su da Ƙabilar Adiyyu Ibn Ka’ab Ibn Lu’ayyu, sukayi kwana da kwanaki akan irin wannan halin, sannan sai Allah SWT Ya É—aura musu tunanin sukai hukunci ga wanda ya girme su mana, shine Abu Umayyah dan Mughira Al-Makhzoomi, sai yace: Yaku Ƙuraishawa to ku yadda wanda ya fara shigo wurin nan daga wannan maganar shi zai É—auki dutsen nan yasa, sai suka yarda, sai suka sa ido suna lura da waye farkon wanda zai shigo, sai ga Annabi Muhammad ne Ya fara shigowa, gaba É—ayansu da suka ganshi sai sukace: shikenan ga amintacce yazo, mun yarda daShi, ga Muhammadu yazo mun yarda❗️

Da Annabi Ya iso gare su sai suka bashi labari, sai ya shimfiÉ—a Mayafi, sai Annabi Ya É—auki wannan dutsen, yasa akan wannan mayafin, yace kowace Ƙabila ta kama gefen mayafin nan, sai yace: to su É—aga, sai suka É—aga shi gaba É—aya har saida suka kai daidai tsawon katangar da za’a sashi, sai Shi Annabi Ya É—auko shi da hannun Shi mai albarka sai yasa, sai Annabi ya zama sababin kiyaye yaÆ™in da yaso ya afku tsakanin su. 

✂️ KuÉ—in ginin Ka’abah yayi wa Ƙuraishawa kaÉ—an game da cika wannan ÆŠaki abisa harsashin Annabi Ibrahim AS, sai ya zama dole ne su rage girman Ka’abah, don haka wannan gini na É“angaren hagu sai sukayi gini akanshi wanda suka barshi a matsayin Katanga gajeruwa, don su sanar cewa shima É“angare ne daga cikin bangaren dakin Ka’abah, shine abunda aka sani a yanzu da (Hijiru Isma’eel), suka É—aga Ƙofar Ka’abah daga Æ™asa, sai suka rage tsawon Ka’abah ta bangaren Gabas shine abunda ake kira da Ash-shadharawan.

*✍ ANNASIHA TV*
(https://twitter.com/AnnasihaTv?s=09)

Post a Comment (0)