BAI HALLATA LIKITA YA AMSHI KYAUTA BA


BAI HALLATA LIKITA YA AMSHI KYAUTA BA

*Tambaya*
Assalamu alaikum, 
Dr. likita ne yayi operation ma wata mata successfully. sai mijin matar yayi masa kyauta.ya hallata ya karba?

*Amsa*
Wa alaikum assalam 
Bai halatta ba, tun da aikinsa ne da yake amsar albashi akansa, Annabi S.A.W. Yana cewa: " Duk Wanda muka ba shi aiki, mu ka sanya Masa Albashi, duk abin da ya amsa bayan haka, ya ci haram" kamar yadda Abu-dawud A rawaito

Allah ne Mafi sani

*Amsawa ✍️ Dr. Jamilu Yusuf Zarewa*

31/01/2021

Daga *ZAUREN FIQHUS SUNNAH*
Post a Comment (0)