ISTIKHARA SUNNAH CE


Alhamdulillah.
Yin Istikhaarah sunnah ce wadda Annabi Sallallahu alaihi wasallam ya umurci dukkan wani mumini da ya aiwatar kafin aikata wani al'amari.

Hadisi ya inganta daga Jabir ibn Abdullah, Allah ya yarda dashi :Manzon Allah (SAW) ya kasance yana koya mana yin Istikhara (neman zabin Allah) a cikin dukkanin al'amura kamar yadda yake koya mana sura daga cikin surorin Alqur'ani. Ya kan ce: Idan dayanku yayi niyyar yin wani al'amari to yayi sallah raka'a biyu ba farillah ba sannan ya ce:

"Allaahumma inni astakheeruka bi ‘ilmika
wa astaqdiruka bi qudratika wa as’aluka min fadlikal adhiim, fa innaka taqdiru wa laa aqdir, wa ta’alamu wa laa a’alam, wa anta ‘allaam al- ghuyoob. Allaahumma fa in kunta ta’alamu haadha’l-amra ( sai ka fadi abin da yake istiharan a kai ) khayran fi deeni wa ma’aashi wa ‘aaqibati amri, faqdurhu li wa yassirhu li thumma baarik li fihi. Allaahumma wa in kunta ta’alamu annahu sharrun li fi deeni wa ma’aashi wa ‘aaqibati amri, fasrifhu anni wasrafni anhu waqdur li al-khayr haythu thumma radini bihi" [Buhari]


Ma'ana da Hausa:
"Ya Ubangijina! ina neman zabinka da iliminKa, ina neman tabbatuwar ikonKa, ina rokan falalarKa Mai gaima, Kai ke da iko ni banda shi, Kai ne Masani ni ban san (komai ba) Kai ne masanin abin da yake boye. Ya Ubangiji na! In kana ganin wannan abu (sai ya fadi abin da yake istiharan a kai) shi yafi min a addinina da rayuwata da qarshen lamarina, to ka tabbatar min da shi, ka sauqaqe min sannan ka yi min albarka a cikinsa, in kuwa kana ganin wannan abu sharri ne gare ni a addinina da rayuwata da qarshen lamarina, ka juyar da shi daga gare ni, ni ma ka juyar da ni daga gare shi, ka qudurtarmin da alkhairi sannan ka amintar min da shi" [Bukhari].

Mustahabbi ne ka nemi shawarar wasu talikai muminai, masu kula da addini, masu gaskiya da kuma riko da addini kafin yin istikhaarah.~ Al-Nawawi.

Duk wanda ya nemi shawarar mutane masu ilimi, gaskiya da riko da addini kuma ya nemi zabin Mahalicci, sa'annan yayi azama a cikin lamarinsa, to ba zai yi nadama ba da yardar Allah. Domin Allah Madaukakin Sarki ya ce: "Kuma ka shawarce su cikin lamarinka, idan kuma ka quduri aniya, to ka dogara ga Allah".

Me ake karantawa a salaatul Istikhaarah?

Anso bayan an karanta Fatihaah, sai a karanta Qul'yaa ayyuhal-kafiroon a raka'ar farko sai kuma Qul huwallaahu ahad a raka'a ta biyu. Dangane da bayanin karanta wadannan surorin Al-Nawawi yace yana da kyau mutum ya karanta su ne saboda ya nuna cewa tabbas yabar lamarinsa ga Allah. Kuma zaka iya karawa da dukkan wata aya daga Qur'aan wadda ta shafi abinda kake neman zabin.


A ina ake karanta wannan addu'ar?
A Mazhabobin Hanafi, Maliki, Shafi'i da kuma Hanbali sunce ana karanta wannan addu'ar ne bayan an idar da sallar. Kamar yadda Hadisi daga Manzon Allah ya tabbatar.. Al-Mawsoo'ah al-Fiqhiyyah. Shaikhul Islam Ibn Taymiyyah yace a cikin Fataawa al-Kubra Kashi na biyu, feji na 265 dangane da karanta addu'ar istikharaah; Mutum yana iya karanta ta gabanin ko bayan sallama. Yin addu'a kafin sallama yafi inganta saboda Manzon Allah sallahu alaihi wasallam yana yin addu'o'insa ne kafin sallama. Saboda haka zaka iya yin addu'a kafin sallama a kowace irin sallah ba sai kawai ta istikhaarah ba.


Yadda ake gane zabin daga Allah;
Ana ganewa ne da yanayin nutsuwar zuciya, sa'annan kuma idan ma idan aure ne sai kajizuciyar ka
ya qara nutsuwa da yarinyar ko saurayin da kike so, idan sana'a ce ma zaka hankalinka ha kwanta akanta.
Za'a iya yin wannan sallah raka'a biyu da rana, ba dole sai da daddare ba, amma anfi son ayi da dare saboda anfi amsar addu'ar bayi a irin wannan lokacin. Haka zalika anso bayan ka gama sallar ka kwanta da alwawa kuma ka fuskanci alqibla. Sannan ka yi tayi ne daga lokaci zuwa lokaci har sai ka sami biyan buqata.
Wallahu A'alamu.

By Ummu Basma
Post a Comment (0)