JAMI'A A TAFIN HANNUNKA 02


JAMI'A A TAFIN HANNUN KA

Kashi Na 02

VISITOR A JAMI'O'IN NIGERIA:-

• Menene Visitor

•Menene amfanin sa a Jami'a

• Wa yake iya zama Visitor
_________________________________________________________________________________

Visitors a Jami'a suna taka rawar gani ne ta hanyar kai ziyara a Jami'ar da kuma fuskantar (Addressing) duk wani matsala da ya gagara a warware (Solver) shi a cikin gida (Within the University), da kuma sauran wadansu ayyuka da doka ta daura a Kansu 

Visitor a Jami'a shine Mamallakin Jami'ar, wato wanda ya kafa ta (Founder)
Shugaban Kasa na wannan lokacin shine Visitor na kowace Jami'a da take mallakin gwamnatin tarayya (Federal Universities), Gwamnoni kuma sune Visitors na Jami'ar da take Mallakin Jihar tasu, (State Universities) a yayin da Private Universities kuma wadanda suka kafa/kirkire ta sune Visitors dinta.

Shi Visitor baya cikin wadanda suke gudanar da harkokin Jami'ar, amma zai ware wani lokacin da zai bibiyi ko yasa a bibiyi abubuwan da suke gudana a Jami'ar, ta hanyar kai Ziyara a Jami'ar (Visitation) domin ya tabbatar da ingancin yadda Jami'ar ke gudana. Sannan ya zama Visitor din yakai ziyarar da kansa ko kuma ya tura wakili akalla a cikin Shekara biyar yaje ko ya tura sau daya.

Visitor a tsarin Jami'o'in Nigeria yana da gindin zama a idon doka.

Misali:
Idan muka kalli dokar da take tafiyar da Jami'ar Ilorin (University Of Ilorin, Act) zamuga Sashi na 13 sakin layi na daya (1) yayi maganar Visitor, inda ya bayyana cewa shugaban kasa Na wannan lokacin shine visitor na Jami'ar, haka ma Sashi na 15 Sakin layi na daya (1) na Kundin tafiyar da Jami'ar tarayya dake Otuoke, da kuma Federal Universities Of Technology, Act, Sashi na 13, Sakin layi na daya (1), hakanan yazo a cikin "The Universities Miscellaneous Provisions, 2003 (Amendment) Act. Sashi na 7AA, Sakin layi na daya (1)
Sannan Sashi na 7 sakin layi na daya (1) na dokar tafiyar da Ahmadu Bello University, Act da Sashi na 14 sakin layi na daya (1) na dokar tafiyar da Bayero University, Act duk sunyi maganar Visitor a Jami'o'in na Nigeria.

• Menene amfanin Visitor ?

Visitor yana da matukar amfani domin kuwa zamu iya cewa kusan shine mai magana ko ra'ayi na karshe (Final Decision) akan abubuwan da suke faruwa a Jami'ar.
A duk lokacin da rikici ko baraka ta faru a Jami'ar wacce aka kasa warwareta to anan ne Visitor zai yi amfani, kamar yadda ya faru kwanakin a baya a Jami'ar Legas, sannan kuma a ziyarar tasa zai kalla abubuwan da Jami'ar take bukata da kuma matsalolin ta akarshe sai ya bawa Jami'ar tabbacin Samar da gyara ko mafita akan haka.

Sannan idan Jami'ar tana fuskantar wani damuwa na cikin gida (Internal Crisis) wanda ya gagareta magancewa ko kuma damuwa daga wajen gida (External Crisis) to kai tsaye zasu tura wannan damuwar zuwa ga Visitor shikuma zaiyi duk abinda ya dace.
Kamar yadda Jami'ar Legas take ta rikici kwanakin baya akan Shugabancin Jami'ar da suka gagara warware matsalar Visitor dinsu suka nema (Wato Shugaba Muhammadu Buhari) shi kuma sai ya nada wakilai akan suje su warware matsalar.

Wannan kadan kenan daga cikin amfanin sa.

Bissalam
12/02/2021
ASOF2021
Arewastf@gmail.com
Post a Comment (0)