JARABAWA CE DAGA UBANGIJI


JARRABAWA CE DAGA UBANGIJI

DUK LOKACIN DA KA SHIGA TSANANI A RAYUWA KAR KA MANTA DA ABUBUWAN NAN

 Ka tuna cewa Jarrabawa ce daga Ubangijinka, wanda yafi kowa Sonka da Kaunarka.

 Ka tuna cewa Ubangijinka yayi maka haka ne don ya Kankare maka Zunubanka, ko kuma ya daukaka maka darajarka.

Ka tuna cewar rungumar Qaddara
kowacce iri, yana daga cikin Ginshikan Imaninka. Gwargwadon yadda kake rungumar Qaddara, gwargwadon haka imaninka yake.

Ka tuna cewa an jarrabi Annabawa da Manzanni da Salihan bayin Allah
wadanda suka zo kafin ka.

Babu wani Annabin da ya rayu salun alun babu wata jarrabawa a rayuwa da Allah ya dora masa, 

Annabi Ayyuba ga kudi ga Annabta, amma babu lafiya, 

Annabi Yakub ga 'ya'ya ga Annabta amma babu kudi, 

Annabi Ibrahim ga Annabta, ga daukaka amma kuma mahaifin sa yana bashi matsala, 

Annabi Nuhu ga imani ga arziki amma matar sa da 'dansa sune babbar matsalar sa a
rayuwa.
.
Asiya Bintu Mazaahim, ga kudi ga daukaka, ga imani, amma ga kafirin miji "Fir'auna", 

Annabi Yusuf ga kudi, ga kyau, ga Annabta amma babu uwa da uba a tare dashi, ga rayuwar gidan yari, ga sharrin Mata.
.
Annabi Muhammad (S.A.W) ga Annabta, ga kyau, ga dimbin magoya baya amma babu wadatan kudi, 

toh idan har zaka rinka bata rai kana fushi akan wasu matsaloli a rayuwa toh da sauran ka a imani, idan har Annabawa basu zauna haka kawai ba duk da tsoron Allah su, da bautan su, toh kai a suwa? ni a suwa?.
.
Dan haka kada ka rinka saka wa ranka cewa wai a rayuwa akwai wani lokacin da zai zo baka da matsala, ba za'a yi haka ba kuma
ba'a taba yi ba, in dai kayi imani da Allah.
ka duba da kyau kaga wani ikon Allah a cikin mutane wani Allah yakan bashi lafiya amma sai a hana shi kudi ko arzikin da zai
rinka walwala dasu, rashin kudin nan sai ya rinka 'daga masa hankali.
.
Wani kuma sai Allah ya bashi kudi amma sai a hana shi lafiyan da zai ji dadin kudin, wani sai Allah ya bashi 'ya'ya masu albarka amma
sai a bar shi babu wadata, 

wata sai Allah ya jarrabe ta da miji mai arziki amma kuma baya nuna ya damu da ita, baya daukar ta da muhimmanci, tana zaune ne kawai domin biyayya da hakuri ba dan tana jin dadi ba, Sai ta rinka tunanin da ace talaka ta samu wanda zai damu da ita, ya so ta ya kauna ce ta, da tayi farin ciki, 

wata Kuma tana chan
tana tunanin ita da me kudi ma ta samu da ta huta, a yayin da wata take auren mai kudin amma tana Allah wadai da kudin tunda baya kula da ita.
.
Dan haka kada kace zaka rayu babu jarrabawa, idan jarrabawar tazo ka roki Allah ya fitar da kai lafiya kawai.

Ya Allah ka yaye mana dukkan Tsanani don son da mukewa Annabi
Muhammad SAW.

SHIN KA KARU DA WANNAN TUNATARWAR IDAN KA KARU TURAWA YAN'UWA MUSULMI.
Post a Comment (0)