Walkiya
Nasiha a Takaice:
✍️ Prof. Mansur Sokoto, mni.
14 Sha'aban 1442H (28/03/2021)
Ma'aunin Jama'a
Sheikh Salman Al-Audá yake cewa: "Da yawa mukan dora kanmu a matsayin ma'aunin jama'a. Idan kana gudu da mota sai ka ga mai tafiya a hankali sai ka ce wawa ne, alhalin wani lokaci kai ma irin tafiyarsa kake yi. Idan wani ya fi ka gudu ya wuce ka, sai ka ce, wannan ba ya da hankali; zai halaka kansa. Idan wani ya yi kyauta kasa da taka sai ka gan shi a matsayin marowaci, idan ya wuce ka kuma ka yi masa kallon almubazzari. A fagen ibada ma duk wanda bai yi daidai da irin ibadarka ba sai ka yi masa kallon wanda bai iya ba ko bai yi daidai ba.
📒 Kuskure ne ka dauka cewa, aikinka shi ne ma'aunin yin daidai ga mutane. Ka tuna cewa, kai kanka rayuwarka da tunaninka da ayyukanka duk canjawa suke yi. Duk abinda wani yake yi a yau, ko dai ka taba yin sa ko kuma a nan gaba zaka yi shi. Mu rika ba jama'a hanzari muna yi masu uzuri".