MAKOFTAKA TA SIYARWA



Nasiha a Takaice
✍️ Prof. Mansur Sokoto, mni.
12 Sha'aban 1442H (26/03/2021)

Makwautaka ta Siyarwa

A wani zamani da ya gabata, wani mutum ya so ya sayar da gidansa. Sai aka kimanta kudin gidan a Dirhami dubu biyu. Amma kuma sai ya ce, shi a dubu hudu ne kawai zai saida gidansa. Aka ce saboda me? Ya ce, lallai kudin gidan dubu biyu ne amma akwai kudin makwautaka da Abu Hamza.
Aka ce masa, ka taba jin an sayar da makwautaka? Sai yace, to idan na ba ku gidan ya zan bar maku makwaucin da, duk sadda na bukaci abu zai ba ni, in na nemi agajinsa ya agaje ni, idan ba ni nan a gidana ya wakilce ni, in na dawo ya taimake ni?!
Da Abu Hamza ya ji wannan takaddama da ake yi sai ya aika masa da Dirhami dubu hudu, ya ce masa manta da su; kada ka sayar da gidanka.
Post a Comment (0)