RANAR JUMA'A


RANAR JUMA'A....

MAFI AKHAIRIN RANAH ITACE RANAR JUMA'A

_Hadisin Imamu Muslim Wadan Aka Samo Daga Abu Huraira [Radiyallahu Anh] Yace Da Kunne Na Naji Ma'aiki [Me Tsira Da Aminchi] Yana Cewa..._

ﺧﻴﺮ ﻳﻮﻡ ﻃﻠﻌﺖ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺸﻤﺲ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ: ﻓﻴﻪ
ﺧﻠﻖ ﺍﺩﻡ ﻭﻓﻴﻪ ﺃﺩﺧﻞ ﺍﻟﺠﻨﺔ ﻭﻓﻴﻪ ﺃﺧﺮﺝ ﻣﻨﻬﺎ ﺭﻭﺍﻩ
ﻣﺴﻠﻢ

_Ma'ana Mafi Alkhairin Yini Da Ranah Ta Hasko/Fito Aciki Itace Yinin Juma'ah, Domin Acikin Ta Allah Madaukaki Ya Halicci Annabi Adam [A.S] Kuma Acikinta Allah Madaukaki Ya Shigar Dashi Aljannah, Sannan Acikinta Allah Madaukaki Ya Fitar Dashi Daga Aljannah.Intahah._

_Hakanan Wani Hadisi Na Daban Wanda Imam Abu Dawood Ya Fitar Da Sanadi Ingantacce Sahabi Aus Ibn Aus [Radiyallahu Ahn] Yace Naji Ma'aiki [Me Tsira Da Aminci] Yana Cewa; Lalle Mafi Falala Cikin Ranaku Itace Ranar Juma'ah, Acikinta Allah Ya Halicci Annabi Adam [A.S] Sannan Acikinta Allah Ya Karbi Tubansa, Sannan Acikinta Za'ayi Busan Qaho [Na Tashin Alkiyama] Sannan Acikinta Har-ila Yau, Za'ayi Tashin Al-qiyama, Don Haka Annabi Yace Ku Yawaita Yi Mini Salati [Acikinta] Domin Salatanku Suna Riska Na,Aus Sai Yace Nan Take Sai Mu [Sahabbai] Mukace Ya Ma'aikin Allah Ta Yaya Salatinmu Suke Iya Riskanka Alhali Ka Riga Ka Kau?Sai Annabi Yace Damu' Lalle Allah Me Girma Da Daukaka Ya Haramta Wa Qasa Cin Naman Annabwa._

ﺇﻥ ﻣﻦ ﺃﻓﻀﻞ ﺃﻳﺎﻣﻜﻢ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ : ﻓﻴﻪ ﺧﻠﻖ ﺍﺩﻡ
ﻭﻓﻴﻪ ﻗﺒﺾ ﻭﻓﻴﻪ ﺍﻟﻨﻔﺨﺔ ﻭﻓﻴﻪ ﺍﻟﺼﻌﻘﺔ , ﻓﺄﻛﺜﺮﻭﺍ
ﻋﻠﻲ ﻣﻦ ﺍﻟﺼﻼﺓ ﻓﻴﻪ , ﻓﺈﻥ ﺻﻼﺗﻜﻢ ﻣﻌﺮﻭﺿﺔ ﻋﻠﻲ .
ﻗﺎﻝ ; ﻗﺎﻟﻮﺍ : ﻳﺎ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﻛﻴﻒ ﺗﻌﺮﺽ ﺻﻼﺗﻨﺎ
ﻋﻠﻴﻚ ﻭﻗﺪ ﺃﺭﻣﺖ? ﻓﻘﺎﻝ ﺇﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﺰ ﻭﺟﻞ ﺣﺮﻡ
ﻋﻠﻰ ﺍﻷﺭﺽ ﺃﺟﺴﺎﺩﺍ ﺃﻷﻧﺒﻴﺎﺀ ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺑﻮ ﺩﺍﻭﺩ ﺑﺈﺳﻨﺎﺩ
ﺻﺤﻴﺢ

SUNNONIN RANAR JUMA'AH....

Acikin Wannan Hadisin Zamu Iya Tsintar Wasu Sannan Sai Mu Hada Da Wasu Wadanda Suma Hadisansu Sun Inganta Misali:

_1-gafara;- Hadisin Sama Ya Tabbatar Mana Da Cewa Acikin Wannan Ranah Aka Gafarta Wa Annabi Adam, Kenan Ranah Ce Ta Neman Gafaran Allah._

_2- Yawaita Salati Ma Annabi Domin Tana Riskansa._

_3- Yin Wankan Juma'a._

_4- Sanya Fararen Tufafi._

_5- Zuwa Juma'a [Masallaci] Da Wuri._

_6- Yin Aswaki._

_7- Yawaita Adduah Awannan Ranah [Domin Dacewa Da Sa'ar Ijaba]._

_8- Ziyartan Yan Uwa Da Abokan Arziki._

_9- Yawaita Azkar Tun Asubahi Har Zuwa Fitar Ranah._

_10- Karanta Suratul Kahfi_


ALLAH YA BAMU IKON AIWATAR DAAU
Post a Comment (0)