TASKAR TARIHI 29


**TASKAR* *TARIHI [29]* 
📌 ```ABUNDA ZAMU AMFANA DASHI DAGA TARIHIN GININ KA’ABAH DA KUMA HUKUNCIN MANZON ALLAH SAW DA YAYI A WAJEN WANNAN JAYAYYA, WADDA TA FARU A TSAKANIN ƘABILUN ƘURAISHAWA``` 
 
1⃣ Yayin da Ƙuraishawa suka zo gina Ka’abah sukace: kar ku shigar da Kuɗi ko kuma dukiya ta haramun, wadda aka same ta daga aikin Karuwanci ko wani zalunci ko Riba. Wannan na nuna mana cewa lallai Larabawa sun riski ƙazanta ta tara Kuɗin riba, don haka suke ƙyamar wannan irin dukiya wajen gina Ka’abah. Ya kamata mu tsaya mu tambaya me zamu ce a yayin da muka ga Larabawa kafin Allah Ya karrama su da ni’ima ta Addinin Musulunci sun san kazanta ta tara Kuɗin Riba, suna kwaɗayin tsarkake al’amura masu muhimmanci daga riba, Me ya samu Musulmi yanzu gashi nan Musulunci na cikin su amma kuma riba tana yawo cikinsu, riba ta wayi gari ta zama wani al’amari ne ma ba abun gudu ba, ba abun ƙyama ba, ya zama a samu wani Musulmi yana da hannun jari a ciki wani Banki ko kuma wani Kamfani wanda wannan Banki ko wannan Kamfani ya mai da riba shine tushen jalin shi.
 
✂️ Ga kafiran Makkah sun haɗu gaba-ɗayansu akan ƙazantar riba, don haka suna ganin aibi ne shigar da dukiyar da suka sameta ta hanyar riba wajen raya Ka’abah, a cikin Al’ummar Musulmi a Yau akwai wanda ya mai da riba itace hanyar cin abincin shi da abin shan shi, ya mayar da ita hanyar ciyar da ƴaƴan shi da kuma basu wurin zama, ba komai bane wannan ba sai Bayahuden Yaƙi ga dukiyoyin mu, don haka dukiya a yau ta wayi gari ta zama rikici har tana mantar da wani Addinin shi, sai kaga yana gabatar da wata hanyar nema wadda take haramun ce ga al’amari wanda yake na Shari’ah ne.
 
2⃣ Ra’ayin nan na taron dangi wanda ya fito daga Ƙuraishawa a halin gasu a zazzaune kewaye da Ka’abah, yayin da Muhammad ya fuskanto gaba-ɗayansu sukace: (mun yarda, amintacce yazo, mun amince, Muhammadu yazo) wannan ra’ayi da suka fadi gameda Muhammad SAW dole ne mu tsayu a wurin wannan ra’ayi muce:
 
✂️ Gamsuwar da Mutane za suyi da Kai yana da matuƙar muhimmanci, sai sun gamsu dakai tukunna sannan zasu saurare ka, don haka cuɗani da Mutane kuma wannan ya baka damar kai kasan su, kayi mu’amala dasu wanann tushe ne ga mai kira zuwa ga Allah, da ace Annabi Ya shiga gare su a wannan Shekaru (a lokacin yana Shekara 35) basu san komai gameda shi ba, da basu yi maraba dashi ba, da basuyi farin ciki da zuwan da yayi gare su ba, Annabi Ya kasance mutum ne wanda ya zama sananne, wanda ya shahara da kyakkyawan ambato a tsakanin su, don yana cikin su din, da kuma kyakyawar cuɗani, da kuma yabo kyakkyawa, Annabi bai kasance mutumin da ya janye jikin shi daga wurin zaman da aka haife shi ba, wanda yaje ya tattaru da kanshi, wanda bai san kowa ba, kuma ba’a san komai gameda shi ba, sannan daga baya yayi nufin ya gyara su, kuma yayi nufin ya samu karɓuwa, yayi nufin samun tasiri cikin su, matakin farko na Mai Da’awah ya kasance a fagen da’awah yana nan dashi ake yin ta, yā sani an san shi kuma yayi ƙoƙarin ya gano muhimmancin cuɗani da jama’ar da yake rayuwa, koda waɗannan jama’ah da yake zaune dasu sun saɓa mishi a Aqeedah.
 
Manzon Allah SAW fa Ya kasance yana mai watsi da duk abunda suke akai na Jahiliyyah kafin a aiko shi ɗin, da sauran abubuwan ƙyama da ƙazanta na Jahiliyya, sai dai kuma bai janye jikin shi daga cikin wadannan Mutane ba, ga duk abunda ya halatta ma sai yayi tarayya dasu, shi Annabi ya san su, sun kuma sun san shi da cewa shi mai gaskiya ne amintacce ne.
 
✂️ Daga cikin mafi muhimmancin sabubba na da’awa wanda suke tasiri, sune ɗabi’u, ɗabi’un Annabi Muhammad su suka sa suke maraba da isowar shi gare su, kuma suke farin ciki da ganin shi, sanann suke murna da kasancewar shine mai raba gardama a tsakanin su, kuma suka yarda dashi tun kafin yayi hukuncin sukace sun yarda, bayan da yayi hukuncin ma sukace sun yarda, wannan shine abunda yake wajibi ga dukkan mai da’awah bambantuwa da kyawawan ɗabi’u da mu’amala wadda take mai falala, domin mutane su san shi, kuma su zo gare shi, sannan su saurare shi su karɓa ra’ayin shi, kuma tasiran su da da’awar shi.

✍ *ANNASIHA TV*
(https://twitter.com/AnnasihaTv?s=09)
Post a Comment (0)