TANADI GUDA GOMA DON SHIGA WATAN RAMADAN 01



TANADI GUDA 10 DAN SHIGA WATAN RAMADHANA


Darasi na farko-(1)

1-TUBA INGANTACCE

*Tuba daga dukkan laifuka da komawa zuwa ga Allah*

Yana cikin gurin mai azumi kafin shiga watan Ramadhana ya*”Ya jaddada tubansa zuwa ga Allah da nisantar dukkan laifuka da komawa zuwa ga Allah”*dan ya shiga watan yana mai tsarki daga dukkan laifuka da kusanci da Allah,dan ya sami lada mai yawa ta azuminsa tare da samun damar aiyukan alkhairi mai yawa.

Amma idan mutum ya shiga yana mai yawan sabon Allah da zunubai,to da wuya ya sami damar aiwatar da aiyukan alkhairi mai yawa a wannan wata mai albarka,sannan ba zai sami cikakkiyar lada da gafara da mai azumi yake samu ba saboda bai bar sabon Allah har acikin Azumi.

Hakika Tuba daga dukkan laifuka wajibi kuma wajibancinsa yana kara karfi a cikin watan Ramadana,domin watane da ba’a so mutum yayi sabon Allah acikinsa.
Allah yana cewa:
*( ﻓَﺎﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻭﻩُ ﺛُﻢَّ ﺗُﻮﺑُﻮﺍ ﺇِﻟَﻴْﻪِ ﺇِﻥَّ ﺭَﺑِّﻲ ﻗَﺮِﻳﺐٌ ﻣُﺠِﻴﺐ *(
@ ﺳﻮﺭﺓ ﻫﻮﺩ ‏( 61 )
*( ﻳَﺎ ﺃَﻳُّﻬَﺎ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﺁﻣَﻨُﻮﺍ ﺗُﻮﺑُﻮﺍ ﺇِﻟَﻰ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺗَﻮْﺑَﺔً ﻧَﺼُﻮﺣًﺎ ﻋَﺴَﻰ ﺭَﺑُّﻜُﻢْ ﺃَﻥْ ﻳُﻜَﻔِّﺮَ ﻋَﻨْﻜُﻢْ ﺳَﻴِّﺌَﺎﺗِﻜُﻢْ ﻭَﻳُﺪْﺧِﻠَﻜُﻢْ ﺟَﻨَّﺎﺕٍ ﺗَﺠْﺮِﻱ ﻣِﻦْ ﺗَﺤْﺘِﻬَﺎ ﺍﻟْﺄَﻧْﻬَﺎﺭُ ﻳَﻮْﻡَ ﻟَﺎ ﻳُﺨْﺰِﻱ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﺍﻟﻨَّﺒِﻲَّ ﻭَﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﺁﻣَﻨُﻮﺍ ﻣَﻌَﻪُ ﻧُﻮﺭُﻫُﻢْ ﻳَﺴْﻌَﻰ ﺑَﻴْﻦَ ﺃَﻳْﺪِﻳﻬِﻢْ ﻭَﺑِﺄَﻳْﻤَﺎﻧِﻬِﻢْ ﻳَﻘُﻮﻟُﻮﻥَ ﺭَﺑَّﻨَﺎ ﺃَﺗْﻤِﻢْ ﻟَﻨَﺎ ﻧُﻮﺭَﻧَﺎ ﻭَﺍﻏْﻔِﺮْ ﻟَﻨَﺎ ﺇِﻧَّﻚَ ﻋَﻠَﻰ ﻛُﻞِّ ﺷَﻲْﺀٍ ﻗَﺪِﻳﺮ *(
@ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻟﺘﺤﺮﻳﻢ ‏( 8 )

Daga Abi Musa R.A Daga Manzon Allah ﷺ Yace:
*(Lallai Allah yana shimfida Hannunsa da dare dan ya karbi tuban wadanda sukayi laifi da rana, Kuma yana shimfida Hannunsa da rana dan ya karbi tuban wadanda sukayi laifi da dare,yana yin hakan har zuwa lokacin da rana data fito daga mafadarta)*
ٌ@ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺃﺣﻤﺪ 4/395 ﻭﻣﺴﻠﻢ 8/99.

Daga Ibn Abas R.A yace:Manzon Allah ﷺ yace:
*(Kutuba ku koma zuwa ga Ubangijinku domin lallai nima ina tuba zuwa garshi a kowane yini sau dari)*
@ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺍﻟﻨﺴﺎﺋﻲ ﻓﻲ ﻋﻤﻞ ﺍﻟﻴﻮﻡ ﻭﺍﻟﻠﻴﻠﺔ‏( 447 ).

Ya yan uwana mu tuba mu koma zuwa ga Allah,domin Allah yana matuqar farincikin da tuban bawansa.
Manzon Allah ﷺ yana cewa:
*(Allah yana farin ciki da tuban bawansa fiye da farin cikin da dayanku zaiyi lokacin da ya rakuminsa ya bata acikin sahara sannan rakumin ya dawo zuwa gareshi sai ya kama igiyar Rakumin yace dan girman farin ciki”Allah kaine bawana nine Ubangijinka……)*
@ﻓﻲ ﺍﻟﺼﺤﻴﺤﻴﻦ.


Allah ne mafi sani.

Mu hadu a darasi na gaba insh Allah.

(* ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺑﺎﺭﻙ ﻟﻨﺎ ﻓﻲ ﺭﺟﺐ ﻭﺷﻌﺒﺎﻥ ﻭﺑﻠﻐﻨﺎ ﺭﻣﻀﺎﻥ )*
Post a Comment (0)