TARIHIN SARKI HAJJAJ BIN ATH THAQAFI


*TARIHIN SARKI HAJJAJ BIN YUSUF ATH THAQAFI*
✍ Mansur Sokoto
2 Janairu 2012

*Bismillahir Rahmanir Raheem*
Hajjaj bin Yusuf wani gwamna ne da aka yi a zamanin halifancin Umawiyyawa. 
An haife shi a shekarar da aka samu hadin kan musulmi; shekara ta 41H Lokacin da sayyidi Al Hasan Dan Ali ya mika ragamar mulkin musulunci zuwa ga sayyidi Mu'awiyah Allah ya yarda da su baki daya.
Hajjaju jikan sayyidina Urwatu bin Mas'ud ne kuma ya yi mafi yawan rayuwarsa a Ta'if inda ya hardace Alkur'ani kuma ya dade yana karantar da shi kyauta ga 'jama'a manya da kanana kamar yadda ya samu mahaifinsa yana yi.
Hajjaju mutum ne mai matukar fasaha da iya magana, ga shi kuma mai yawan kyauta da kauce ma Jin dadi. Amma akwai tsanani a tare da shi.
Farkon shahararsa shine Lokacin da sarki Abdulmalik bin Marwan ya lura da kaushin halinsa sai ya tura shi zuwa Makka inda ya yaki Abdullahi bin Zubair ya karya mulkinsa a shekara ta 73H. 
Daga bisani sai aka mika masa ikon Hijaz (Makka da Madina da Ta'if) inda ya raya wadannan garuruwa matuka. Ya samar da rijiyoyi, ya gina masallatai, ya kyautata ma talakawa. Bayan haka sarki Abdulmalik ya kara masa da mulkin kasashen Yemen da Yamamah.
Daga nan kuma sai aka tura shi Iraqi don ya shawo kan kungiyar KHAWARIJ da kuma tawayen 'yan Shi'ar Kufa a shekara ta 75H.
Iraqi dai wuri ne da ya yi fice a wancan lokaci wajen yawan bore da tashin hankula da rashin da'ar talakawa. Hajjaju ya yi amfani da kaifin takobi ya dallashe kaifin wadannan mutane. Amma fa ya wuce gona da iri. Kuma ya tauna tsakuwa sosai, ba aya ba har gyada da su wake ma sai da suka ji tsoro.
A shekarun 81-83H Hajjaju ya yi fama da yakin basasar da Ibnul Ash'ath ya jagoranta inda ya karya lagon 'yan tawayen, ya mayar da doka da oda ga kasa.
Bayan haka ne ya shelanta ci gaba da jihadi don isar da sakon musulunci a matsayinsa na gwamna mai iko a wannan yankin inda ya ci manyan garuruwan kafirai da ke tsallaken teku. A wannan lokacin ne addinin musulunci ya isa kasashen Pakistan da Indiya da wasu yankunan Rasha wadanda suka hada har da Bukhara da Samarqanda. Manyan kwamandojin da Hajjaju ya yi amfani da su sun hada da Qutaiba bin Muslim Al Bahili wanda yakokansa suka dangane har da birnin Sin (kasar China). Da kuma dan baffan shi Hajjajun; Muhammad bin Al Qasim Ath Thaqafi, Wanda yake karamin yaro ne dan shekara 17 amma bai san gudu ko ja da baya ga yaki ba.
An sifaita Hajjaju da zama azzalumi, maras tausayi, mai rashin yafewa. Saboda ya ci zarafin bayin Allah mutanen kirki da dama da malamai wadanda kaddara ta sa su shiga cikin yakin basasar da muka ambata.
Duk da haka kuma an fadi cewa ya yi hidimar Alkur'ani sosai har ana jinjina masa a wannan fage.
Mulkinsa dai ya fi kama da mulkin soja saboda tsananin dokokin da yake aiwatarwa. A lokacin rikonsa ne ya hana bayyana kukan mutuwa wanda ya zama wata mummunar al'ada a wancan lokaci, ya tsananta doka a kan giya da sata, ya kuma hana tsugunawa don biyan bukata a wuraren da jama'a ke wucewa.
Ta fuskar siyasa kuma ya buga sababbin kudi, ya fitar da sabon kundin tsarin aikin gwamnati duka da manufar larabtar da su bayan a da ana amfani da su da Farisanci. Sannan ya kula da sha'anin noma da raya karkara inda ya sa aka samar da wadataccin ruwa domin manoma, ya samar da shanun noma kuma ya ba manoma rance.
Tun a cikin kuruciyarsa Hajjaju ya yi karatu ga sahabbai irin su Ibnu Abbas Da manyan tabi'ai irin su sarkin malamai Sa'id bin Al Musayyib. Don haka kulawarsa da Alkur'ani ba ta yi rauni ba a lokacin da ya zama mai mulki. Don haka zamu ga tarihi ya tabbatar masa da lambar girma wajen hidimar Alkur'ani. Shine dai mutum na farko da ya fara sa a wasalce Alkur'ani, a rubuta masa digagga, a banbanta farkon sura da kaloli. Kuma ya fitar da Hizibi da Nisifi da Rubu'i da Thumuni don saukake ma masu harda da masu taqara. Ya kuma ware albashi na musamman ga mahardata da makaranta Alkur'ani.
Hajjaju ya auri 'yar gidan Abdullahi bin Ja'afar bin Abi Talib, sai dai an yi ta kai da kawo a kan auren har aka raba su saboda nuna cewa bai cancanci ya aure ta ba.
'Yan Shi'a sun zargi Hajjaju da kisan sharifai, amma maganarsu ba ta da tushe, domin gaba daya a zamanin mulkin 'ya'yan Marwan ba wanda ya ke taba Hashimawa balle ya tozarta su ko ya kashe su. Babu shakka ya kashe mutane da dama, kuma Allah zai yi masu hisabi da shi amma dai ba dangin Annabi ba Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam.
An ce lokacin da mutuwa ta zo ma Hajjaju ya rinka cewa, Ya Allah! Ka gafarta mani. Hakika duk mutane suna ganin ba zaka iya ba!
Hajjaju ya rasu a karshen watan azumi na shekara ta 95H yana da shekaru 54 a duniya. Ya mutu a garin Wasit, kuma duk abin da ya bari bai kai Dirhami 300 ba, abin da bai wuce wani sarki ya yi kyautarsa ga karamin mutum ba.
Ana iya duba tarihinsa a cikin TARIKH AL UMAM WAL MULUK, na Tabari, Juz'i na 3 da AL BIDAYA WAN NIHAYA, Juz'i na 9 da MURUJ ADH DHAHAB na Mas'udi, Juz'i na 3 da AL KAMIL na Ibnu Adiy, Juz'i na 1. Akwai kuma littafan da aka wallafa kan tarihinsa kamar AL HAJJAJ BIN YUSUF: LIL HAQIQATI ALFU WAJHIN, na Ahmad Tammam da ALHAJJAJ BIN YUSUF AL THAQAFI AL MUFTARA ALAIHI, na Dr. Mahmud Ziyadah.
Sheikhul Islam Ibnu Taimiyyah ya yi maganarsa a wurare da yawa a littafansa, kamar JAMI'UL MASA'IL (4/157) da MINHAJUS SUNNATIN NABAWIYYAH (2/36) da (4/348) da KITAB AR RAD ALAL MANDIQIYYIIN (1/502) da kuma AL JAWAB AS SAHIH LIMAN BADDALA DIN AL MASIH (5/264) da sauransu. Kuma maganganun Ibnu Taimiyyah suna cike da adalci da tacewa tare da la'akari da yanayi da zamanin da ake magana a kan sa.
Ya Allah ka ba mu ikon yi ma tarihinmu nazari na adalci da gaskiya.
Post a Comment (0)