BA YA HALASTA AYI KASUWANCI DA KUƊIN BASHI


*BA YA HALATTA AYI KASUWANCI DA KUDIN ADASHI*

Tambaya
Assalamu Alaikum Dr, ina da tambaya kamar haka
Mace ce ta shirya adashi wanda za'a dunga zubi har tsawon shekara daya ko makamancin haka, sannan kudin da mutane ke bata na zubi tana sayan kaddarori da kayan ajiya ko sana'a irin su kaji, POS, sayarda kayan sanyi da makamantar haka, da niyyar kada kudaden mutane su narke, cewa idan shekara ko lokaci ya zagayo zata saida ta ba su abin da suka zuba. Shin hakan ya halatta alhali kayannan da ta sayo zai yiwu ta yi riba ko ta fadi alhali masu kudi basu da kaso ko hasara ciki?  

Allah Ya kara ma Doctor lafiya, basira da nisan kwana.

Amsa
Wa alaikumus salam 
Bai halatta ba, saboda ka'ida sananniya a Sharia "Ba a sarrafa dukiyar wani sai da izninsa"
Al'ada tana da tasiri a zamantakewa, ana komawa zuwa gare ta idan aka samu sabani wajan fahimtar HUKUNCI.

A Al'adar Bahaushe Adashi ajjiya ce kawai ba tare da sarrafawa ba, don haka bai halatta ayi kasuwanci da kudin amana ba sai da iznin mai shi .

Allah ne Mafi sani

Amsawa.. 
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

08/03/2021


Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)