ZAN IYA YIN SALLAH A ZAUNE SABODA ƘATON CIKI?


*ZAN IYA YIN SALLAH A ZAUNE, SABODA KATON CIKI ?*

 *Tambaya:?*

Assalamu Alaikum warahmatullahi wa barakatuhu Malam . Inada tambaya Ina da tsohon ciki, idan ina sallah
sunkuyo da tashi yana bani wahala zan iya yi azaune ?

  *Amsa:*

Wa alaikum as salam, Zaki iyayi a zaune, in har ba za ki iyayi a tsaye ba,saboda hadisin Imran dan Husain lokacin da ya fadawa Annabi(SAW) Basir din da yake
damunsa, sai ya ce maşa : “Ka yi sallah a tsaye,in ka kasa ka yi a zaune, in ka kasa yi a zaune kayi a gefenka”, kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 1066. Hadisin daya gabata yana nuna cewa: wanda yake da
lalurar da zata hana shi yin sallah a tsaye, zai iya yi a zaune, saboda addinin musulunci mai
sauki ne, ba ya dorawa rai abin da ba zai iya
ba. 

Allah shine mafi Sani.

*Amsawa*✍🏻

*Dr.Jamil Yusuf Zarewa*
16/04/2017
Post a Comment (0)