*TASKAR TARIHI [26]*
📌 _FALALAR KHADIJAH (RA)_
1⃣ Manzon Allah SAW ya ce: “ _*mafi alherin Mata a zamanin Banu Isra’il; Maryam ƴar Imran, sannan mafi daraja daga cikin Matan wannan zamani na al’ummar Annabi Muhammad SAW, itace Khadijah."*_ [Bukhaariy da Muslim].
Imamun Nawawiy yace: (ma’anar wannan Hadisi shine: kowace ɗaya cikin waɗannan Mata itace mafi alherin Matan zamanin ta, dangane da fifiko tsakanin Maryam da kuma Khadija, wannan abu ne wanda yake Shari’a tayi shiru akai, don haka abunda yafi alheri kai ma kayi shiru akai).
2⃣ Daga Nana Aishah (RA) ta ce: duk matan Manzon Allah SAW ba wadda nake yiwa Kishi sai Khadijah, amma fa Ni ban taɓa ganinta ba, saboda Annabi Ya kasance idan ya yanka Akuya sai yace: *“kufa aika wa ƙawayen Khadijah”,* wataran sai na baShi haushi nace: wai wacece Khadijah ne? sai Manzon Allah SAW yace: “ *Ni an azurta Ni da sonta ne”* [Muslim: Hadisi na 2435].
Imamun Nawawiy yace: (wannan nuni ne akan cewa son Khadijah ma daraja ce wadda ta samu ga Annabi SAW, kamar shine ya samu daraja da yake son ta).
3⃣ Abu Hurairah (RA) ya ce: " *wataran Mala’ika Jibrilu yazo wa Annabi SAW yace: Ya Manzon Allah! Ga Khadijah nan zata zo maka da Kwano a cikin Kwanon akwai Miya da Abinci, da abunsha (Faranti ɗauke da haɗaɗɗen Abinci), idan Khadijah ta iso gare ka, kace Ubangiji yana gaishe ta kuma gaisuwar daga gare Shi ce, Nima Mala’ika Jibrilu ina gaishe ta, sannan kayi mata albishir da Gida a Aljannah na Ƙarau (Lu’Lu’ wanda yake fafaffe), babu Kwarmaniya a cikin gidan sannan babu wahala"* [Muslim].
Khadijah RA itace fa tayi Imani da Manzon Allah SAW lokacin da Mutane suka Kafirce miShi, kuma ta gasgata Annabi lokacin da Mutane suka ƙaryata Shi, ta taimake Shi da Dukiyar ta lokacin da Mutane suka hana Shi, ita kaɗai ce daga cikin Matan Shi ta haifa mishi Ƴaƴa.
Ibnu Hajar yace: (daga cikin darajojin da Khadijah take ɗauke dasu, ta riga kowa Imani cikin Mata, sai ya zama ta Sunnanta ma duk wata Mace da zata dawo tayi Imani da Annabi har Duniya ta tashi, to Khadijah tana da ladan wannan Mata domin Khadijah ce ta fara Imani daShi, saboda ya tabbata a Hadisi Annabi ya ce: “wanda ya fitar da kyakyawar Sunnah” ta ɓangaren Maza Abubakar Siddiq shine ke tarayya da ita, ba’asan iya ladan da kowani ɗaya daga cikin su suke dashi ba, saboda wannan Imani na farko, ba wanda yasan yawan ladan su sai Allah (SWT).
✍ *ANNASIHA TV*
*Twitter*👇🏼
https://twitter.com/AnnasihaTv?s=09
*WhatsApp* 👇🏻
https://wa.me/2348142286718?text=Assalamu%20Alaikum%20Zan%20So%20Na%20rika%20samun%20aiyukan%20AnnasihaTv.%0A%0