*TASKAR TARIHI [27]*
```📌 FA’IDOJIN DA ZAMU SAMU GAMEDA KISSAR AUREN MANZON ALLAH SAW DA KHADIJAH RA```
1⃣ Hakika dama ita Khadija ta riga taji Labarai masu yawa gameda Gaskiyar Manzon Allah SAW, da kuma Amanar Shi, sai ta aika miShi yazo yayi mata Kasuwanci, ta haɗa shi tare da Yaronta mai suna Maisarah, sai wannan Yaro ya dawo yana bata labarin abubuwan Gaskiya da ya gani ido da ido na Amana da kyawawan ɗabi’u, wannan na nuna mana cewa Matar nan tana da kaifin hankali, hakan yasa tayi gaggawar ta fara mu’amala da Manzon Allah SAW yayin da taji labarin amanar Shi, sannan kuma ta ƙara gamsuwa da amanar Shi da gaskiyar Shi yayin da Maisarah ya bata labari, wanda yayi tafiya tareda Manzon Allah SAW, a wannan lokacin tafiya yaga Gaskiya da Amana.
Ita tafiya itace take yaye haƙiƙanin halin Mutum, itace take fito da ɗabi’un shi wadanda suke a boye. Mai Da’awah ya kamata ya kwaikwayi hali na saurarawa da bin abubuwa sannu-sannu irin yadda Khadijah tayi da rashin gaggawa.
2⃣ Wannan lamari na Khadijah na tunsasshe mu gameda Maɗaura auren Ƴaƴa Mata su rinƙa kwaɗayin aurar wa da Mutanen kirki Ƴaƴansu, koda ta hanyar yin Tallar(gabatar da) Ƴaƴan ne, kaga dai wanann Aure na Khadijah itace ta gabatar da kanta ga Annabi SAW amma ta samu daraja mai girma, ta wayi gari ta zama Matar mafi darajar halitta a cikin halittu, ta zama uwar Muminai.
Na daga cikin haƙƙin da Ƴaƴanmu Ƴan Mata suke dashi akan mu, da Ƴan’uwan mu Ƴan Mata, muyi ƙwazon samo musu Mazaje, Garurukan mu na Musulunci da Anguwannin mu na Musulmi na cike da ƴan Mata riƙaƙƙu waɗanda suna nan babu Aure, sakamakon cewar shi Uban ko kuma shi Babban wansu dukansu basa wani kataɓus wajen binciken samo musu Samari nagari, sai dai kuma wajibi ne ga Mutum ya kyautata hanyar da zai bi wajen gabatar da Yar shi ko Yar’uwar shi ga wanda yake so, ya kamata a gabatar da ita wannan Yarinya ne ta hanyar da zata kiyaye mutuncin Yarinya da kuma mutuncin danginta, saboda kada yazo ya wulaƙanta ta daga baya.
3⃣ Lallai wannan Aure na Khadijah da Manzon Allah SAW akwai darasi da muke iya ɗauka gameda muhimmancin zaɓen da ya kamata Namiji yayi ga Matar Aure ta gari, da kuma irin yadda Mace ya kamata ta zaɓi Miji na gari, ta girme Shi da Shekara 15, tayi aure kafin shi har sau biyu tare da haka sai Annabi SAW ya zaɓe ta a matsayin ta zamar miShi Mata, saboda tsarkin ta da kuma kamewar ta.
Ita Khadijah ɗin nan manya-manyan Mutane daga cikin Kuraishawa, suna ta zuwa wurinta domin su aure ta, duk da haka tayi watsi dasu, amma da taga ɗabi’u maɗaukaka da Siffofi na yabawa gameda Muhammad SAW sai tayi kwaɗayin ya zama Mijin ta kuma tayi fatan Allah Ya tabbatar mata da haka.
_Don haka shi Namiji Manzon Allah ne abun koyin shi wajen zaɓan Mace, ita kuma Mace Khadijah itace abar koyinta wajen zaɓar Miji._
4⃣ Khadijah RA ta samar da Gida ga Annabi SAW idan ya samo matsalar da’awah shine wurin da yake zuwa ya fake, wannan ya ishemu mu dubi matsayin da Khadijah ta ɗauka a ranar farko daga cikin ranakun da aka fara aiko da Annabi SAW, sanda yace mata Ni ina jin tsoron kada wani abu ya same Ni, don ina jin naga Aljani ne, kada ya taɓa mun hankali, tace dashi: ( *ko ɗaya, na rantse da Allah Ni Khadijah, har abada Allah bazai Wulaƙanta ka ba)* , haƙiƙa Annabi SAW yakan dawo gida ahalin an cutar dashi, idan ya dawo sai ya samu ga Matar da zata kwantar mai da hankali a Gida, ta ƙara mishi ƙarfin damatsa, ta tabbatar dashi akan abunda yake cewa daidai ne, bata kasance Mace mai zargi ba, wacce take karkatacciyar gameda da’awar da Annabi yake zuwa ga Allah.
Sannan kuma duk Matar da ta nuna irin wannan hali na goyon baya, sai a samu matsayi irin na Manzon Allah tare da ita shine cikakken cika alƙawari, don haka yana yawan ambaton Khadijah bayan rasuwarta, kuma yana sadar da zumunci da danginta, har Aishah RA tana kishin Khadijah.
✍ *ANNASIHA TV*
*Twitter* 👇🏿
https://twitter.com/AnnasihaTv?s=09