*WASIYYAR UBA CIKIN HIKIMA*
*✍️ Yusuf Lawal Yusuf*
Akwai wani mutum da ɗansa ƙarami. Kullum cikin dare yakan riƙa yi masa wa'azi a sha'anin zama sa mutane. Tun yaron bai balaga ba sai Allah ya yi wa uban rasuwa. A ranar ƙarshe kafin ya mutu sai ya ce da ɗansa, "Wataƙila ciwon nan nawa ba na tashi ba ne. Saboda haka akwai wasiyyoyi da nake so in gaya maka amma zafin ciwo ba zai bari ba. Don haka in na rasu ka je wajen tsohon doki da kiyashi da kumurci da kare za su gaya maka abin da zan gaya maka." Yana gamawa sai ya rasu.
Bayan an gama zaman makoki sai yaro ya niyyata ya tafi wurin tsohon doki ya gaya masa saƙon mahaifinsa.
Tsohon doki ya ce," Lallai mahaifinka ya yi maka wasiyya mai kyau. Ka gan ni a nan ko turkena ba a share ba. Har yanzu ban karya kumallo ba. Ruwan sha sai na yi haniniya a kai-a kai ake tunawa da ni. Wai kawai domin na tsufa. Lokacin ƙuruciyata ba abin da ba a yi min. In an hau ni ina nagarta har fitowa ake yi ana kallo na, ana guɗa. Amma yanzu ina! *(1) Don haka komai za ka yi, ka yi lokacin ƙuruciyarka.* Wannan shi ne dalilin wasiyyar mahaifinka. Sauka lafiya."
Daga nan yaro bai zarce ko'ina ba sai wajen kiyashi. Ya gaya masa saƙon ubansa. Kiyashi ya ce," Lallai akwai wasiyya kuwa. Biyo ni ka ga abin da yake nufi. Suna cikin tafiya sai suka yi kaciɓis da mushen kyankyaso. Kiyashi ya ce, "Ka ga wannan mushe babu shakka ya raba ni fiye da ɗari a girma. Saboda haka ba zan iya jan sa in kai ramina ba, bayan kuma ina so saboda abincina ne. " Yaro ya ce, "I, gaskiya ne."
Kiyashi ya ce, "Tsaya ka gani." sai ya je ya kirawo kiyasai Æ´an'uwansa rututu. Nan da nan suka gewaye mushen kyankyaso suka ja giriri har cikin raminsu. Yaro ya ce, "To, me ke nan? " Kiyashi ya ce, *(2) "Komai za ka yi kada ka yi kai kaÉ—ai sai da jama'a, jama'ar, kuma taka.* Wannan shi ne wasiyyar mahaifinka."
Yaro ya yi godiya ya tafi wurin kare, ya gaya masa abin da ke tafe da shi.
Kare ya ce, "Zo mu je." Kare ya wuce gana yaro yana biye har suka zo wata makarantar allo mai almajirai da yawa an hura wuta ana ta karatu.
Daga tsayawarsu sai aka fara jifan kare ana, "Kolo", "Kolo". Da ƙyar suka tsere. Ba su tsaya a ko'ina ba sai gidan wani mafarauci. Daga ganin kare sai aka ba shi abinci, aka goge masa jiki, aka ɗaura masa fata a wuya. Kare ya ce da yaro, "To ka gani, lokacin da muke je makaranta ba a yi wata wata ba sai aka kore mu; amma da muka zo gidan mafarauci ga irin alherin da aka yi mana. *(3) Saboda haka komai za ka yi a duniya ka yi tare da masoyinka a inda ake son ka."*
Yaro ya yi sallama da kare ya tafi neman inda kumurci yake. Da ƙyar ya same shi a cikin wani kogon kuka. Ya gaya masa abin da ya kawo shi.
Kumurci ya ce," Babu shakka babanka mutum ne mai tsinkaya. Yanzu ka gan ni nan a É“oye. Ba na fita da rana. Kuma ko daddare sai an yi barci don in ba haka ba da an gan ni sai a bi ni da duka a kashe ni. Ka san dalili?
Yaro ya ce, "A'. Kumurci ya ce, "Harshena da bakina, su suka jawo min wannan bala'i. *(4) Don haka ka kiyayi harshenka da bakinka.* Abin da babanka yake son gaya maka ke nan." Yaro ya yi godiya ya yi sallama ya tafi.
Daga: Littafin Hikayoyin Kaifafa Zukata, littafi na É—aya (1),wallafar Malam Aminu Kano Rahimahullah.
*18th Rajab, 1442A.H (02/03/2021).*