YA WAJABA A MAYAR DA HAƘƘI ZUWA GA MAI SHI


*YA WAJABA A MAYAR DA HAKKI ZUWA GA MAI SHI*

*Tambaya*
Assalamu alaikum Allah shi-Gafarta Malam. Tambayata anan itace, Ma'aikacin Banki idan yayi kuskuren amsar Short ko Jabun Kudi sai ya biya. To Malam. Idan Ma'aikacin Banki ya samu Over a cikin kudi Ya halatta a gare shi ya yi amfani da su??

*Amsa*
Wa alaíkum assalam
Ya wajaba ya mayar da kudin ga Mai shi , tun da akwai lambar wayar shi da kuma adreshinsa da lambar gidansa a wajansu, Allah Yana cewa a cikin suratun Nisa'i (Allah Yana umartarku ku mayar da hakkoki zuwa ga ma'abotansa).
Cin dukiyar wani ba da san ransa ba haramun ne, duk jikin da ya ginu da Haramun wuta ce ta fi cancanta ta lamushe shi.

Allah ne mafi sani

*Dr. Jamilu Yusuf Zarewa*

24/02/2021


ZaKu iya Bibiyar Mu a 

Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)