WATAN SHA'ABAN DA BIDI'O'IN DA AKA ƘIRƘIRO


WATAN SHA'ABAN DA BIDI'O'IN DA AKA KIRKIRA A CIKINTA.

✍️ Rubutawa: Najeeb Elkabir Kwarbai

Hadisi ya inganta daga Nana A'isha (RA) Ta ce:

لم يكن رسول الله صلى الله عليه وسلم يصوم في شهر أكثر من شعبان، فإنه كان يصوم شعبان كله. و في رواية: كان يصوم شعبان إلا قليلا.

"Annabi SAW bai kasance a yana azumtar wata wata ba fiye da sha'aban, domin ya kasance yana azumtar dukka watan. A wani ruwayar kuma yace: " Ya kasance yana azumtar Sha'aban gabakidaya sai yan kwanaki kadan (ne baya azumtarsu).

Wani ruwayar kuma Ya zo daga Usama ɗan Zaid (RA) ya ce: Na cewa Annabi SAW:

لم أراك تصوم شهرا من الشهور ما تصوم من شعبان، قال: "ذلك شهر يغفل الناس عنه بين رجب و رمضان، و هو شهر ترفع فيه الأعمال إلى رب العالمين، فأحب أن يرفع عملى و أنا صائم".

"Me yasa na ga kake yawan azumi a cikin watan Sha'aban fiye da sauran watanni? Sai Ya ce: " Wannan watan shine watan da mutane suka gafala a kansa tsakanin Rajab da Ramadan. Kuma wata ne da ake ɗaukaka ayyukan bayi a cikinsa zuwa ga Ubangijin talikai, saboda haka shi yasa nake so a daga ayyuka na a lokacin ina azumi".

BIDI'O'IN DA AKE A CIKIN WATAN SHA'ABAN.

Akwai hadisi da Imam Turmidhi ya ruwaito da yake cewa:

"إن الله عز و جل ينزل ليلة النصف من شعبان إلى السماء الدنيا فيغفر لأكثر من عدد شعر غنم كلب"
"Lallai Allah Mai Girma da BuwayaYana saukowa saman duniya a tsakiyar watan Sha'aban, sai ya gafartawa da yawa daga cikin mutane, wanda adadinsu ya kai yawan gashin tunkiya".

MENE NE HUKUNCIN WANNAN HADISIN?

Imamu Turmidhi Ya ce:

و سمعت محمدا (يعني البخاري) يضعف هذا الحديث.

"Na ji Muhammad (Yana nufin Bukhari) yana raunana wannan hadisin.

Da kuma Hadisin:

إذا كانت ليلة النصف من شعبان فقوموا ليلها و صوموا نهارها"

"Idan daren rabin watan Sha'aban ya kasance, ku yi sallah a cikin daren, kuma ku azumci yininsa".

MENE NE HUKUNCIN WANNAN HADISIN?

" و في الزوائد: إسناده ضعيف لضعف ابن أبي بسرة و قال فيه أحمد و ابن معين يضع الحديث"

Ya zo a cikin littafin Al- Zawa'id: Isnadin hadisin yana da rauni, saboda raunin Ibnu Abiy Basrah. Imamu Ahmad da Ibnu Ma'in sun ce yana kirkiran hadisai.

Saboda haka babu wani hadisi da ya zo ƙarara yake nuni a kan falalan daren rabin watan Sha'aban (Nisfu Sha'aban).

Daga cikin bidi'an da ake yi a wannan watan, sallah mai raka'o'i shida a cikin daren rabin watan, da niyyar tunkude bala'i ko tsawon rayuwa ko wadatuwa da abin da yake hannun mutane, da karanta Suratul Yasin da yin addu'a a lokacin, kai wannan aiki ma ya saɓawa Sunnar Annabi SAW, kuma kirkirarren al'amari ne a cikin addini.

Mai Sharhin littafin Al-Ihya Yana cewa:

" Wannan sallar (ta tsakiyar watan Sha'aban) ta shahara a cikin litattafan Sufaye na karshe-karshe. Ni ban ga wani isnadi ingantacce da ya nuna halascinta ba, ko kuma akwai wani addu'a da ake yi a lokacin, sai dai kawai Shehunnai ne suka kirkiro ta suke aikatawa. Mutanenmu sun ce: Makaruhi ne a hadi a irin wannan daren da aka ambata a cikin masallaci ko wani wuri. Najamul Gaidiy yana cewa game da siffar yadda ake raya daren da taron jama'a: Ya ce wannan aikin da yawa daga cikin Malamai na Hijaz daga cikinsu akwai Ada'u da Ibnu Mulaika da Malaman fikihu na Madina da Almajiran Malik duk sun yi inkarin haka, suka ce: Wannan aikin gabakidaya shi bidi'a ce , babu wani abu da ya inganta daga Annabi SAW game da tsayuwar dare a cikin jama'a na hadisi, haka bai inganta ba zuwa ga Sahabbai Allah Ya kara musu yarda.

Imamu Nawawiy yana cewa: "Sallar da ake yi a watan Rajab da Sha'aban dukkanninsu bidi'o'i ne munana".

Haka nan akwai wadanda suka wuce iyaka a kan watan, har suka ce ai daren rabi watan Sha'aban shi ne daren lailatul qadar, babu shakka wannan maganar karya ce, babu gaskiya a ciki. Abin da ke nuna rashin gaskiyan zancen shi ne hadisai ingantattun da suka zo a cikin Sahihul Bukhari da Muslim da suke nuna cewa daren lailatul qadar yana a kwanakin goman karshe na watan Ramadan ne.

Allah Yasa mu dace.
Post a Comment (0)