YAYA AKE RAMUKON AZUMI GA MAMACI?


*YAYA AKE RAMUKON AZUMI GA MAMACI?* 

https://chat.whatsapp.com/IZhc4HXjGXFDOuOmx3ceZA

 *TAMBAYA* ❓

Assalamu Alaikum. Malam ya dawainiya da al'umma da taimako wajen fahimtar dasu akan abin daya shige musu duhu. Allah ya karawa malam hakuri da juriya da mutane. Ameen.
Malam tambaya ta anan itace 'mutum ne ya kai shekaru hudu da rasuwa kuma ana binshi bashin Azumi, yaran shi basu biya mishi azumin da ake binsa ba, amma dangin shi suke so su biya mishi'. To yaya azumin zai kasance kenan wajen ramukon? 


 *AMSA* 👇

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Lallai akwai hadisi Sahihi wanda Manzon Allah (saww) yace : "DUK WANDA YA MUTU DA AZUMI AKANSA, TO WALIYYINSA YAYI MASA AZUMIN".
To amma Malamai s unyi ma hadisin fahimta daban daban.
Misali :
Wasu daga cikin Maluman Hadisi da kuma Abu Thaur sunce ya halatta Waliyyin mutum (wato Makusancinsa) yayi masa azumi amadadinsa, saboda hujjar wannan sahihin Hadisin.
Maluman Ahlul Baiti da Imamu Malik da Abu Hanifah sun ce ba za'ayi azumi amadadin Mamaci ba. Abinda ya za wajibi shine aciyar da Miskini guda bisa kowanne azumi guda da ake bin Mamacin. Sun kafa Hujjah da Hadisi Sahihi wanda Imamut Tirmidhiy ya ruwaito daga Sayyiduna Abdullahi bn Umar (ra) :
"WANDA YA MUTU DA AZUMI AKANSA, TO ACIYAR DA MISKINI GUDA BISA KOWACCE RANA".
(Ibnu Maajah ma ya ruwaito irinsa acikin Sunanu nasa, kuma Hadisi ne Sahihi).
Abinda ke Qara Qarfafar wannan shine Fatawar da aka samu daga Sayyidah A'ishah da kuma Ibnu Abbasin (ra) akan cewa ciyarwar za'ayi.
Ibnu Qudaamah yace Wannan ita ce Sahihiyar Fatawar Mafiya yawan Ma'abota ilimi. Kuma an ruwaito haka daga Nana A'ishah da Ibnu Abbas (ra). Kuma ita ce Fatawar Maliku da Layth bn Sa'ad da Auza'iy da Sufyanuth Thawree da Shafi'iy da Hasan bn Hayyin da Ibnu 'Ulayyah da Abu Ubaidin acikin Sahihiyar Magana daga garesu.

WALLAHU A'ALAM.

Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕
Post a Comment (0)