*`````🌲 Ahlul Qur'anاهل القران* 🌲 *```*
*FATAWA AKAN AURE*
======================
_*ZUWA GA AMARYAR GOBE*_
======================
*_Tambaya_* :
Assalaamu alaikum wa rahmatul laah.
Mallam Ni budurwa ce Kuma gobe za a daura mini aure zan zama amarya, wacce shawara za a bani da kuma wasiyya?
*_Amsa_* :
Wa alaikumus salamu wa rahmatullahi wa barakatuh.
Shawarar da za'a baki bata da yawa kuma bata da amfani har fa sai idan zaki aiki da ita. Da farko dai, ki yi hakuri, domin aure ibadah ne, kuma ba wata ibadah dake yiwuwa sai da hakuri. Ki zamo mai tsoron Allah da taķawa, hakan bai samuwa sai da zuwa makaranta. Don haka ki maida hankali wajen neman ilmi. Ki zan mai cikakkiyar biyayya ga Annabi kafin ga mijin ki. Haka ki so mijin ki, amma ki fifita son Allah da Manzo a kan son sa. Ki sani wannan zama na aure da duk abinda zai haifar ibadah ne. Ki zamo mai biyayya ga mijin ki har ki fifita biyayyar ki a kan ta iyayen ki, biyayyar Allah da ta Manzo kadai ke fin ta shi a matsayin sa na mijin ki. Ki girmama iyaye, yan uwa da aminan sa. Ki zamo mai yawaita addu'ar alkhairi gare shi a ko da yaushe. Ki zamo mai wadatuwa da duk abinda ya iya baki, sannan ki gode masa. Ki kula da tsabta da canja girki mai dadi a kai a kai. Ki ji, ki yi kamar baki ji ba, ki gani kiyi kamar baki gani ba. Ki guji almubazzaranci da tozarta masa dukiya ko abin ci in ya kawo, ki zamo mai tattali. Ki zamo mai raha a labarin ki da shi. A wannan farko zaman na ku, ki kokarin gane abin da yake so, ko ki tambaye shi, da irin abinda baya so don ki guji yi masa su da ganganci.
Kar ki dinga bashi labarin kawayen ki. Ki guji kai labarin ku na sharri, a wurin yan uwa ko iyayen ki. Kina da damar farun albarkacin bakin ki, amma da kin hararo zai koma musu, toh ki kame bakin ki. Haka a lokacin sabani da bacin rai, ki koyi bashi hakuri. Ki zamo mai taimakon mijin ki da karfin ki da dukiyar ki. Ki zamo mai tausayin mijin ki. Mijin ki ya zamo abokin shawarar ki ba wanin sa ba.
Daga karshe kar ki dauko salon zaman wasu ma'aurata ki kawo gidan ki, sai na alkhairi. Wannan kadan ne daga cikin abin da za'a baki na Shawara.
Wallahu ta'ala a'lam.
*21/1/2021*
*_Amsawa_* :
*Malam Aliyu Abubakar Masanawa*
*_Gabatarwa_*
*:Lukman Musa Eloquent*
*_Daga_*
*Zauren Ahlul Qur'an* ,
Ga masu son shiga tura sunan ka/ki da number ta WhatsApp.
0903 364 6444