HALASCIN KALLON MATAR DA KAKE SO KA AURA

HALASCIN KALLON MATAR DA KAKE SON AURA

HADISI ya Tabbata Manzon Allah (ﷺ) Yana Cewa:

عن جابر بن عبد الله قال : قال رسول الله صلى الله عليه وسلم : ( إذا خطب أحدكم المرأة فإن استطاع أن ينظر إلى ما يدعوه إلى نكاحها فليفعل ) 
{أبو داود: ١٨٣٢}

 An Kar6o Daga Jabir Bn Abdallah (ra) Yace: Manzon Allah (ﷺ) Yace: {Idan Ɗayanku Yama Neman Mace da Auren Mace, Idan Ya Samu Daman Kallon Abinda Zai Sanya Masa Son Aurenta To Ya Kalla}.
(Abu-Daud: 1832)

Imam Shafi'i (RH) Yana Cewa: (Idan Mutum Zi Auri Mace Ne, To Ya Halatta Ka Kalli Fuskarta da Tafukan Hannunta Kaɗai)
(Al-Hawy Al-Khubra:9/ 34)

Ibn Ãbidin Yana Cewa: (Ya Halatta Ka Kalli Fuskar Matar da Kakeson Aura da Tafukan Hannunta Da Kuma Diddigen Ƙafarta. Baya Halatta Kallon Wurin da Waɗannan ba)
[Hashiyatu Ibn Abidin: 5/325).

Har Wa Yau Imam Ahmad (RH) Yana Cewa: {Ya Halatta A Kalli Abinda Galibi Yake Bayyana a Jikinta. Kamar Wuyanta da Hannunta da Makamantansu. Ibn Ƙudama (RH) Ya Hikaito Hakan a Cikin Littafinsa Al-Mugny: 7/454).

YA ALLAH MAZAN DAKE NEMAN MATA KA AZURTASU DA MATA NAGARI. HAKA KUMA MATAN DA BASU DA AURE KA BASU MAZA NAGARI.

✍🏽Abu-Aysha Al-Maliky

Post a Comment (0)