_*HUKUNCIN GAJARTA SALLAMA (Slm) DA HAMDALA (Alhm)*_
https://chat.whatsapp.com/IQUc0RxgCwA3JFiEKl8j5E
*TAMBAYA*❓
Assalaamu Alaikum warahmatullah
Allah ya karawa malam lafiya da ilimi mai amfani.
Malam da Allah menene hukuncin abbreviating sallama,hamdala da kuma rantsuwa a shari'ah? Misali...slm,wlh da alhdl?
Allah ya saka da alkhayri
*AMSA*👇
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuh. Alhamdu lillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu ala rasulillah wa ala alihi wa sahbihi ajma'in.
Tabbas amfani da abbreviation ko kuma shortform na kalmomi abu ne da ya zamo ruwan dare a duniyar musulmi, har ya kai ga jumloli da sunan Allah da salatin Annabi duk basu tsira ba a hannun masu yin hakan.
Ko shakka babu yin amfani da taƙaita sunan Allah, salati, sallama da ababen da suke ibadah ne, bai halatta ba, duba da wasu dalilai kamar haka.
Misali, idan mu ka ɗauki sallama, addu'a ce, ibadah Sunnah ce da Annabi sallallahu alaihi wa sallama ya koyar mana a lafzance da rubuce. Don haka duk wanda ya zo da saɓani haka ya munana biyayya ga Annabi kuma yayi Bid'ah. Lokacin da Annabi ya rubuta takarda zuwa ga wasu sarakuna bai taƙaita sallama ba, bayan bismillah, da shi da mai rubuta masa, babu wanda yayi abbreviation na kalmomi ballantana jumloli da aka yi amfani da su.
2820 - 1294 - «بسم الله الرحمن الرحيم من محمد عبد الله ورسوله إلى هرقل عظيم الروم سلام على من اتبع الهدى أما بعد; فإني أدعوك بدعاية الإسلام أسلم تسلم يؤتك الله أجرك مرتين فإن توليت فإن عليك إثم الأريسيين و {يَا أَهْلَ الْكِتَابِ تَعَالَوْا إِلَى كَلِمَةٍ سَوَاءٍ بَيْنَنَا وَبَيْنَكُمْ أَلَّا نَعْبُدَ إِلَّا اللَّهَ وَلا نُشْرِكَ بِهِ شَيْئاً وَلا يَتَّخِذَ بَعْضُنَا بَعْضاً أَرْبَاباً مِنْ دُونِ اللَّهِ فَإِنْ تَوَلَّوْا فَقُولُوا اشْهَدُوا بِأَنَّا مُسْلِمُونَ} » .
(صحيح) ... [حم ق ت] عن أبي سفيان. مختصر مسلم 1122.
Na biyu, yana haifar da rashin fahimtar saƙo, misali, ana amfani da AA, A/A, SLM, ASAK, duk waɗannan ba zasu bayar da ma'ana ba a musulunce ko a al'ada ba.
Bayan haka shari'a ta tabbatar da cewa zuwa da cikakkiyar sallama yana da ƙarin lada da fifikon falala a kan wanda bai da cikakkiya ba, toh ina ga wanda yazo da abin da shari'a bata san da shi ba?
عَنْ عِمْرَانَ بْنِ حُصَيْنٍ قَالَ جَاءَ رَجُلٌ إِلَى النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَقَالَ السَّلاَمُ عَلَيْكُمْ. فَرَدَّ عَلَيْهِ السَّلاَمَ ثُمَّ جَلَسَ فَقَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: ((عَشْرٌ)). ثُمَّ جَاءَ آخَرُ فَقَالَ السَّلاَمُ عَلَيْكُمْ وَرَحْمَةُ اللَّهِ. فَرَدَّ عَلَيْهِ فَجَلَسَ فَقَالَ: ((عِشْرُونَ)). ثُمَّ جَاءَ آخَرُ فَقَالَ السَّلاَمُ عَلَيْكُمْ وَرَحْمَةُ اللَّهِ وَبَرَكَاتُهُ. فَرَدَّ عَلَيْهِ فَجَلَسَ فَقَالَ: ((ثَلاَثُونَ)).
Idan irin amfani da irin wannan hanya ta taƙaita kalmomi ta shafi abin da yake ibadah kamar sallama, salati, a nan mutum ya zo da abin da Annabi bai umarni da shi don haka yayi Bid'ah, Annabi
5970 - «من أحدث في أمرنا هذا ما ليس منه فهو رد» . الصحيحة 2302: تخ.
(صحيح) [ق د هـ] عن عائشة. غاية المرام 5.
A wata riwayar
6398 - «من عمل عملا ليس عليه أمرنا فهو رد» .
(صحيح) [حم م] عن عائشة. مختصر مسلم 1237، غاية المرام 5، الإرواء 276.
Idan kuma ma irin wannan taƙaita kalmomi ya shafi sunan Allah ne, toh ya zamo ilhadi, iyazhan billahi. Ya kira Allah, a rubuce, amma da sunan da Allah ko Manzo bai kirayi kan sa da shi ba, wannan babban laifi ne a musulunci, har Allah yace game da su,
(وَلِلَّهِ ٱلۡأَسۡمَاۤءُ ٱلۡحُسۡنَىٰ فَٱدۡعُوهُ بِهَاۖ وَذَرُوا۟ ٱلَّذِینَ یُلۡحِدُونَ فِیۤ أَسۡمَـٰۤىِٕهِۦۚ سَیُجۡزَوۡنَ مَا كَانُوا۟ یَعۡمَلُونَ)
[Surah Al-A'raf 180]
Daga ƙarshe dai, mu gane cewa rubutu, zance ne, kuma Allah zai kama da laifukan abin da muka faɗi da harsunan mu ko kuma muka rubuta da hannayen mu. Don haka ragi ko ƙarin harafi a cikin abinda ya shafi sunan Allah ko abin da ya shar'anta, ilhadi ne, Allah yace dangane da haka
(إِنَّ ٱلَّذِینَ یُلۡحِدُونَ فِیۤ ءَایَـٰتِنَا لَا یَخۡفَوۡنَ عَلَیۡنَاۤۗ أَفَمَن یُلۡقَىٰ فِی ٱلنَّارِ خَیۡرٌ أَم مَّن یَأۡتِیۤ ءَامِنࣰا یَوۡمَ ٱلۡقِیَـٰمَةِۚ ٱعۡمَلُوا۟ مَا شِئۡتُمۡ إِنَّهُۥ بِمَا تَعۡمَلُونَ بَصِیرٌ)
[Surah Fussilat 40]
Duk waɗannan wasu nau'ukan tarko ne da dabarar sa da yake amfani da ita wajen ƙawata mana laifi mu dinga ganin ba laifi bane ko kuma babu komai a kai, kamar yadda yayi alƙawali, har mu dinga ganin wanda baya yi, a matsayin kidahumi, bai waye bane, ko kuma ya cika matsantawa a addini
(قَالَ رَبِّ بِمَاۤ أَغۡوَیۡتَنِی لَأُزَیِّنَنَّ لَهُمۡ فِی ٱلۡأَرۡضِ وَلَأُغۡوِیَنَّهُمۡ أَجۡمَعِینَ)
[Surah Al-Hijr 39]
Ya jama'ar musulmi mu faɗaka, mu faɗakar, idan har zaka iya ɗaukar lokacin ka wajen rubuta abinda bai kai sallama, salati ko sunan Allah daraja ba, toh babu abin da zai hana ka rubuta sunan Allah cikakke.
Wallahu ta'aala a'lam.
*_Amsawa_* :
*Malam Aliyu Abubakar Masanawa*