*HUKUNCIN SHAN MAGANIN TAURI !*
Tambaya
Assalamu alaikum Allah ya karawa Dr. Lafiya.
Mene ne hukuncin shan maganin tauri wato Maganin karfe ko kauranci a musulunci ?
Amsa
Wa alaikum assalam
Mutukar babu abin da ya sabawa sharia a ciki, ana iya amfani da shi saboda neman kariya, saboda duk mua'amalolin da mutane suke yi, in har ba'a samu nassin da ya haramta ba, to sun halatta saboda Ka'idar: الأصل في الأشياء الإباحة.
Da yawa daga cikin magungunan tauri akwai kauce hanya a ciki, akwai wadanda ake barin sallah idan an sha, ka da aje garin-neman-gira a-rasa- IDO.
Mutukar maganin tauri ya kunshi abin da sharia ta haramta, bai halatta ayi amfani da shi ba, Biyayya ga Allah maganin KAU-DA-BARA.
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
25/03/1440
03/12/2018
Zaku iya bibiyar mu a
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml
Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi
WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248