HUKUNCIN HAƊA SALLAH SABODA SANYI


HUKUNCIN HAƊA SALLAH SABODA SANYI 

https://chat.whatsapp.com/IZhc4HXjGXFDOuOmx3ceZA

 *TAMBAYA* ❓

Assalamu Alaikum
Shin ko limamai wadanda suke hada sallah saboda sanyi sunada wata hujja ne a shara'a???


 *AMSA* 👇

Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu

Toh zan iya cewa Eh sunada hujjah duk da cewa Mafi yawan Malamai suntafi akan cewa ba,a hada sallah saboda sanyi. Wannan shine abunda Malikiyya da Hanafiyya da Shafi'iyya suka tafi akai. Amma Mazhabar Hanabila sune suke ganin ana iya hada sallah saboda sanyi amma suma sun gindaya wasu sharudda. Daga cikin Sharuddan sukace yazama ba tsurar sanyi akeyiba domin shi sanyi tsurar sanyi idan kasaka riguna ajikinka zaka maganceshi, sukace dole kafin ahada sallar se idan ana wata irin iska wacce ta sa6awa al'ada wacce ita iskar take horo sanyi tana cutarda mutane to anan sukace ana iya hada sallah saboda ita. Sun dai kawo wasu sharuddanda wadannan sune muhimmai, sauran sharuddan basuda muhimmancin sosai. Kuma amma duk da cewa anan muma munada ra'ayin cewa idan sanyin ya haduda irin wannan iskar kuma akaji sanyin yana neman ya wuce al'ada kamar irin wanda akayi kwanaki uku bayan anan kaduna da wasu garuruwa to ana iya hada sallah sabodashi amma sedai kafin ahada din to wajibine se anfara karantarda mutane, musamman kuma dayake karatun yanada nisa sosai ba kowanne littafi bane zakaga ankawo bayani akan batun hada sallah saboda sanyi seka tafi manyan littafai irinsu Fathu Zuljalali wal ikram da irinsu Sharhul Mumti su Almajmu da sauransu wadanda littafaine da sunyiwa karamin dalubi nisa sosai dan haka akwai bukatar karantarwa sosai kafin akaiga aikatawa gaskiya domin tunkude 6arna shine abun gabatarwa akan a jawo amfani.

Allah Yasa mudace
 
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ. 

Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕
Post a Comment (0)