HUKUNCIN WANDA AKA TILASTA SAKI


HUKUNCIN WANDA AKA TILASTA SAKI 

https://chat.whatsapp.com/IZhc4HXjGXFDOuOmx3ceZA

*TAMBAYA*❓

assalamu'alaikum

ina wuni mlm ya qoqari.ALLAH yasaka muku alkhairi. malam dan ALLAH inada tambaya. uwa ta tirsasama dan ta saiya saki matarshi.se dan ya saki matar. to mlm wannan yamatsayin matar akwai sakin kokuma bata sakuba. ngd allah yaqara basiri

*AMSA*👇

Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu

Hakkin iyaye na daya daga cikin manyan hakkoki da Allah Ya yi magana, haka aure na daga cikin sunnar kowane Annabi da Allah Ya aiko bisa doron kasa, har Annabi SAW yake cewa “ Aure sunnah ta ne kuma duk wanda ya kyamace ta ba ya tare da ni”.

Amma duk da girman wannan hakki na iyaye Allah Bai rataya saki a hannun su ba.

Sakin mutumin da aka tilasta; 
Dole ne miji ya kasance mai ra’ayin kansa, idan kuma har wasu za su yi amfani da matsayi na jini ko kusanci ko kuma karfi na mulki a bisa tilasci a sakar wa mutum mace to ba ta saku ba, ciki har da iyaye.

Sai dai mafi kyawu a duk lokacin da mahaifan mutum suka nuna masa ba su son wani abu, sai ya bi hanyar da ta dace don fahimtar da su ta yadda za su amince da abin in kuma har suka cije a kan sai ya yi abin sai ya dubi girman darajar su da suka yi silar samar da shi a bisa doron kasa ya yi masu biyayya don neman yardar Allah.

Don haka ina kira ga iyayen da suka aukar da irin wannan saki da mazajen da aka sakar wa matan da ma wadanda suka aura da dukkanin al’ummar musulmi da mu ji tsoron Allah sannan mu tuntubi malamai, don gaskiya akwai ganganci kuma za a rika afkawa cikin zina da gangan.

Da fatan Allah Ya shiryar da mu bisa tafarki na kwarai. 

Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕
Post a Comment (0)