HUKUNCIN SADUWA DA MACE MAI JININ HAILA?



HUKUNCIN SADUWA DA MACE MAI JININ HAILA?

https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfqds

*TAMBAYA*❓

Slm...mlm meye hukuncin wanda y sadu d matarsa alokacin tana cikin haila


*AMSA*👇

Mai haila damai jinin biki bai halattta saduwa dasu ba, haramunne mutum yasadu da matarsa tana cikin jinin haila ko nifasi, domin Allah madaukakin sarki yace:
ﻭﻳﺴﺄﻟﻮﻧﻚ ﻋﻦ ﺍﻟﻤﺤﻴﺾ ﻗﻞ ﻫﻮ ﺃﺫﻯ ﻓﺎﻋﺘﺰﻟﻮﺍﻟﻨﺴﺎﺀ ﻓﻲ ﺍﻟﻤﺤﻴﺾ ﻭﻻ ﺗﻘﺮﺑﻮﻫﻦ ﺣﺘﻰ ﻳﻄﻬﺮﻥ ﻓﺈﺫﺍ ﺗﻄﻬﺮﻥ ﻓﺄﺗﻮﻫﻦ ﻣﻦ ﺣﻴﺚ ﺃﻣﺮﻛﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺇﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻳﺤﺐ ﺍﻟﺘﻮﺍﺑﻴﻦ ﻭﻳﺤﺐ ﺍﻟﻤﺘﻄﻬﺮﻳﻦ . ﺍﻟﺒﻘﺮﺓ ﺍﻷﻳﺔ ‏( 222 )
Suna tambayarka dangane da jinin haila kace musu kazantane ku kauracewa matayenku lokacinda suke cikin jinin haila, kada ku kusancesu harsai sunyi tsarki, idan sukai tsarki kuje musu ta inda Allah ya umarceku, Allah yanasan masu yawan tuba kuma yanasan masu tsarki.
Bai halatta ga miji yajewa matarsa ba lokacinda take cikin jinin haila harsai tayi wanka tayi tsarki, sannan zai iya zuwa mata.
Haka mai jinin biki lokacinda take cikin jinin bikin, matukar jinin yana zuwa, idan tai wanka tai tsarki yahalatta yasadu da ita, koda bata cika kwana arba'in ba, domin jinin biki bashi dawani lokaci da'aka iya kance masa, tana iya yin tsarki akwana ashirin tana kuma iya yin tsarki akwana talatin, tana kuma iya tsarki sama haka ko kasa dahaka, duk lokacinda tai tsarki mijinta zai iya saduwa da ita, amma lokacin jini bai halatta ba, idan tacika kwana arba'in wajibine agareta tai wanka taitsarki koda jinin yana zuwa,
Idan jini yaci gaba dazuwar mata har tsawon kwana arba'in, to ta cika lokacin jinin bikinta, wajibine tai wanka koda jinin yana zuba, zatai sallah tai azumi wannan jini zata daukeshi amatsayin nacuta, bazai hanata azumi ko sallah ba, kuma bazai hana mijinta yasadu da itaba.
Idan mutum ya sadu da matarsa tana cikin jinin haila ko nifasi hakika ya aikata mummunan laifi, kuma zunubi babba cikin manyan zunubai, wajibine yatuba, kuma kaffara tawajaba agareshi amafi ingancin maganganun malamai, shine rabin dinare daya ko dinare daya, yai sadaka dashi ga mabukata.
Amma idan darashin sani, ko mantuwa, ko jahiltar hukuncin babu komai akansa.
Imamun Nawawi acikin sharhin sahihu muslim ( 3/204) yace:
Idan yakasance da mantuwa yayi ko bashi da masaniyar hailar, ko kuma baisan hukuncin hakan ba, ko kuma tursasashi akai babu komai akansa babu kaffara akansa, idan kuma yasadu da ita da gan-gan, yasan tana haila kuma yasan haramcin saduwar, da zabinsa yayi, hakika ya aikata babban zunubi daka cikin manyan zunubai, wajibine yatuba,
Shaik bin usaimin rahimahullah acikin sharhin mumti'i ( 1/571) yace:
Kaffara bata wajaba akan wanda yasadu da matarsa tana cikin haila ko nifasi saida sharudda.
1- Yakasance yasan da hailar
2- Yakasance yasan haramcin saduwar
3- Yakasance dazabinsa yai saduwar ba tilasta masa akai ba.
Idan yajahilci haramcin, Ko hailar, ko mantuwa, ko tursasa matar akai, ko kuma hailar tazo suna cikin jima'in to babu laifi akansa kuma babu kaffara akansa.
Wallahu A'alamu.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻻ ﻋﻠﻢ ﻟﻨﺎ ﺇﻻ ﻣﺎ ﻋﻠﻤﺘﻨﺎ ﺇﻧﻚ ﺃﻧﺖ ﺍﻟﻌﻠﻴﻢ ﺍﻟﺤﻜﻴﻢ .

Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕

1 Comments

  1. Gaskia ban gamsu ba. Don naji ance za a ba da sadakan 20k shine hukuncunsa shi wanda ya sadu da matarsa yana jini haila. Ya kamata aqara fadada mana bincike.
    Tambaya ta an an.
    Meye hukuncin wanda aka kamashi da laifin yin caca?! Shin ko yanada haddi akan hakan?! Sanna meye haddin nasa?;
    أفيدونا أفادكم الله

    ReplyDelete
Post a Comment