HUKUNCIN WANDA BA YA GAMSAR DA IYALINSA SABODA AZUMIN NAFILA


*MENE NE HUKUNCIN WANDA BA YA GAMSAR DA IYALINSA SABODA AZUMIN NAFILA?*

https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfqds

*TAMBAYA*❓

Assalamu alaikum Malam barka da warhaka, wani bawan Allah ne yake azumin Litinin da Alhamis, ga shi yana shiga hakkin matarsa wani lokachin, tayimishi magana amma yace shi ba zai daina ba so yake ya saba da azumin, komai zaifaru sai dai ya faru, malam azumin ko sauke hakkin matarsa? Allah ya kara daukaka mlm na gode.

*AMSA*👇

Wa'alaikumus Salamu, Tabbas yana daga cikin haqqoqi na wajibi na ma'aurata a kan junansu sauke wa juna haqqin aure ta ɓangaren saduwa, kuma rashin cika wannan haqqin na iya sa ɗaya daga cikin ma'aurata ya kusanci saɓon Allah ta hanyar zina musamman idan aka samu raunin imani, ko kuma hakan ya haifar da mutuwar aure ma baki ɗaya.
Shi kuma yin azumin Litinin da Alhamis sunnah ce daga cikin sunnonin Manzon Allah ﷺ , saboda haka ya sauke wajibin iyalinsa a kansa shi ne a gaba akan yin azumin nafila, saboda katange matarsa ga aikata abin da bai dace ba, kamar yadda yake faɗin komai zai faru ya faru, wannan magana tasa kuskure ne.
Saboda rashin gamsar da juna a tsakanin ma'aurata kaɗai na iya haifar da faruwar fitinar da ba za a iya shawo kanta a tsakaninsu ba in ba ta wannan hanyar gamsarwar ba. Saboda haka sai ya rage yin azumin a kai a kai ko da ba zai daina ba gaba ɗaya tun da yana son koyi da sunnah, kuma ita kanta gamsar da iyali akwai lada a cikinta, kamar yadda azumin taɗawwu'i yake da lada.
Idan kuma ya qi ji, to ta yi haquri da shi akan hakan, saboda kada matsawarta a gare shi ya haifar da wata fitina a tsakaninsu, matuqar dai ba kusantarta ne ba ya yi baki ɗaya ba.
Allah ne mafi sani.
*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*✍🏻

Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕
Post a Comment (0)