HUKUNCIN WANDA KE MUZANTA MUSULMI
https://chat.whatsapp.com/IQUc0RxgCwA3JFiEKl8j5E
*TAMBAYA*❓
Slm mlm inada tambaya!!! Mlm minene hukuncin wanda yake kiran wani da suna jahili kuma dolo alhalin baya daya daga cikinsu, ya fada ne domin ya muxantashi a cikin mutane kawai?
daga Abdullahi bunya
*AMSA*👇
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu
Bai halatta ga Musulmi ya chutar da dan uwansa musulmi ba. Allah yace "WADANDA KE CHUTAR DA MUMINAI MAZA DA MUMINAI MATA, BA TARE DA WANI LAIFIN DA SUKAYI BA, HAKIKA SUN DAUKAR (WA KANSU) WANI ABUN KUNYA DA KUMA LAIFI BAYYANANNE"
Manzon Allah ï·º yace "DUKKAN MUSULMI AKAN MUSULMI, HARAMUN NE JININSA DA DUKIYARSA DA MUTUNCINSA. YA ISHI MUTUM SHARRI ACHE YA WULAKANTA 'DAN UWANSA MUSULMI"
Yazo acikin hadisai cewa duk wanda ke chutar da Musulmai da harshensa, aranar Alkiyamah Allah zai azabtar dashi ta hanyar sanya masa kumban Qarfe ahannayensa sannan ya rika kwaye naman fuskarsa da wadannan Faratan dake jikin yatsunsa. (Allah shi kiyayemu)
Wanda ya tuba tun anan duniya, Allah zai gafarta masa. Amma sai ya nemi yafiya awajen wadanda ya zalunta. kamar yadda
WALLAHU A'ALAM.
Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕