HUKUNCIN YIN AIKI A BANKI



HUKUNCIN YIN AIKI A BANKI 

https://chat.whatsapp.com/JLojawdOWYsEOeSHZMNdjf

 *TAMBAYA* ❓

asalamu alaikum mallam hamisu
na kasance mai aiki a unionbank na wata shida a shekara sai na huta na wata shida , ba a biya na salaryidan ina hutu. to kwanakin baya na saurari wani scholar yana bada fatawa cewa babu kyau musulmi yayi aiki a banki wai koda aikin security ne. haramu ne saboda akwai haramci a ayukan da banki keyi kaman bayar da bashi kuma abiya da kudin ruwa 
help me out saboda yanxu lokaci ya kai wanda zan koma bakin aiki amma ina tsoron ciyar da iyali na da

 *AMSA* 👇

Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu

Indai irin bankunan da suke amfani da kudin ruwa ne, to bai halatta kayi aiki acikinsu ba. Ta kowacce fuska.
Hujjah anan ita ce Hadisin Jabir bn Abdillah Al-Ansary (ra).
"Manzon Allah (saww) ya tsinewa mai cin Kudin ruwa, da mai bayarwa, da mai rubutawa, da mai shaidawa. Yace Dukkansu daidai da daidai suke acikin laifin (zunubin).
(Sahihu Muslim, Hadisi na 1598).
Acikin Sharhin da yayi ma wannan hadisin, IMAMU SHARAFUDDEEN AN-NAWAWY (rah) yace:
"Wannan hujjah ce Qarara wacce take nuna haramcin yin aikin rubutu ko shaidawa acikin duk wata hulda tsakanin mutum biyu masu cinikin kudin ruwa. Kuma ya nuna haramcin taimakawa wani acikin Aikata sa'bon Allah".
Babu makawa duk mutumin da yake aiki a irin wadannan bankunan dole ne zai taka rawa acikin harkar kudin ruwa.
Ko mai gadi ne, ko mai shara ne, ko Clerk ne. Sannan kuma dole ne abiyashi albashi da kudin ruwa.
Don haka gara ka nemi wani aikin mai tsafta.
"Duk wanda yaji tsoron Allah, to Allah zai sanya masa Mafita. Kuma zai azurtashi ta inda ba ya zato. Duk wanda ya dogara da Allah, to shi Allah din zai isar masa"
(Suratul-Talaq ayah ta 2 - 3).

Wallahu a'alam.

Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕
Post a Comment (0)