MIJINA YA KASANCE YANA DUKANA DA ZAGINA



MIJINA YA KASANCE YANA DUKANA DA ZAGINA

https://chat.whatsapp.com/IQUc0RxgCwA3JFiEKl8j5E 

*TAMBAYA*❓

Slm Barka da yammah
Mijina Yakasance Yana dukana da zagina agaban Yaranmu ko kuma Yace seya sakeni To malam ya aurenmu yake 
Sannan zan iya neman saki 
Sannan Allah zesakamun dukan dayakemun ko kuwa ba sakayyah

*AMSA*👇

Wa alaikumussalaam Wa Rahmatullahi Wa Barakaatuh. In dai a yanda ki ka yi bayani hakan abun yake, to lallai zagin mutum musulmi da wulakanta shi haramun ne sannan yana daga cikin manyan laifuffuka, shi yasa Manzon Allah(SAW) yace a hadisin da ya zo cikin Sahihul Bukhari da Sahihu Muslim da Sunan daga Abdullahi dan Mas'ud (سباب المسلم فسوق وقتاله كفر), Shiyasa wannan bã dabi'ar Annabi ba ne (SAW), kamar yadda hadisi yazo daga A'ishatu (Allah Ya kara mata Yarda), tace Manzon Allah(SAW), bai taba dukan wani abu ba da hannun shi , haka bai taba dukan mace ba ko ma'aikaci(mai hidimah) sai dai idan a halin yaki ne, sannan wani bai taba yi mishi wani abu ba kuma ya dau fansa daga gareshi ba sai dai idan an keta wani abu daga abinda Allah Ya haramta sai yadau fansa saboda Allah(SWT), saboda haka wajibi ne kowane namiji ya kyautata wa matar shi wajen zamantakewa ya dinga yi mata kyakykyawan mu'amala kamar yadda Allah (SWT), yayi umarni da hakan cikin Suratunnisa'i :(وعاشروهن بالمعروف),Wato Kuyi Zamantakewa da su da alheri da kyautatawa.
Shiyasa Mallamai ma'abota ilimi sunyi bayanin ya halasta ga mace idan tana fuskantar zalunci da cutarwa daga mijinta babu laifi ta nemi saki daga gareshi,wasu suna ganin wajibi ne ma ya sake ta in dai ta nemi sakin, sannan bayan ya sake ta kuma aladabtar da shi , Khalil yace a cikin littafin shi(مختصر):
( ولها التطليق بالضرر ولو لم تشهد البينة بتكرره), 
Idan kuma ya ki sakin ta to zata iya yin khul'i (الخلع),amma dukan da shari'ah ta yadda da shi shine yake kasancewa yayin da mace take kangarewa mijinta bata mishi ladabi da biyayya, shima yana halasta ne bayan ya mata nasiha Idan bata ji nasihan ba(batayi aiki da shi ba), to hali na biyu sai ya kaurace mata wajen bacci(ya nesance ta wajen bacci), idan wannan bai yi anfani ba sannan yake halasta ya dan duke ta amma da wadannan sharuddan:
(1) Dukan ya kasance kadan ba mai yawa ba.
(2) Kada ya duke ta a fuska.
(3) Kada ya zageta a lokacin da yake dukan ta.
(4) Idan ta daina lefuffukan da takeyi, sai ya daina irin wannan dukan.
والله تعالى أعلم.

*DR NASIR YAHYA ABUBAKAR BIRNIN GWARI*

‎Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
 *_Group Admin: ▽_*
 *MAL. HAMISU IBN YUSUF*
Post a Comment (0)