HUKUNCIN YIN SHAFA AKAN SAFAR QAFA (SOCKS)



HUKUNCIN YIN SHAFA AKAN SAFAR QAFA (SOCKS)

https://chat.whatsapp.com/IZhc4HXjGXFDOuOmx3ceZA

 *TAMBAYA* ❓

Assalamu Alaikum. Malam da Fatan Kana Lapia Tare da Iyali. Allah ya taimaka. 
Malam Ya Halaschin Shafa a kafa Yake Lokachin da Mutum Ya Sanya Safa Bayan Daura Alwala. Bayan Ya Fita Kuma sai Fitsari Ya Kama Mutum Lokachin Sallah, Ya Halatta Yayi Shafa a Kafar sa yayin sake wata Alwalar? Anyi Fitsari amma Ba'a cire safar ba, Kuma sai a sake alwala Kuma akayi Shafa sannan Kuma akayi Sallah.


 *AMSA* 👇

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Bisa Mazhabin Imamu Malik (Rahmatullahi alaihi) shi yace bai halatta ayi shafa akan safar Qafa. Da kuma duk abinda aka yishi da tsumma. Shi awajensa ba'a yin shafa sai dai akan Huffi na fata, ko kuma bandeji (ga masu rauni ko miki).
Haka shima abu Haneefah yace bai halatta ayi shafa akan safa ba. Sai dai daga baya ya dawo daga kan wannan fatawar kafin rasuwarsa da kwanaki uku ko bakwai.
Amma Imamu Ahmad da Imamush Shafi'iy da sauran Maluman Fiqhu irin su Sufyanuth Thauree, Auza'iy, da sauransu, duk suna ganin halascin yin shafa akan safa.
Imam Abu Dawud ya lissafo sunayen Manyan Sahabbai wadanda aka ruwaito cewa sunyi shafa akan safar Qafa. Acikinsu akwai Imamu Aliy bn Abi Talib (karramal Lahu wajhahu) da Ibnu Mas'ud, Al-Bara'u bn Aazib, Anas bn Malik, Abu Umamah, Sahlu bn Sa'ad, Amru bn Huraith, Sayyiduna Umar bn Al-Khattab, Abdullahi bn Abbas, Ammar bn Yasir, Bilal bn Rabah, Abdullahi bn Abi Awfa (Yardar Allah ta tabbata akansu baki daya).
Amma kafin yin shafar ya halatta gareka Malamai sun gindaya sharudda kamar haka :
1. Ya zamanto Safar tana da kauri yadda ba'a ganin fatar Qafarka ta cikinta.
2. Ya zamanto ta rufe maka sawayenka har zuwa idon sawu.
3. Ya zamanto ka sanyasu ne bayan kayi tsarki kayi alwala cikakkiya.
4. Ya zamanto ka sameta ne ta hanyar halal. Imamu Ahmad yace bai halatta kayi da safar da aka sato, ko aka kwace daga wajen mai ita ba.
Siffara yadda akeyi kuma, zaka sanya tafin hannunka na dama daga sama, na hagu kuma daga Qasa sai ka shafo daga yatsunka zuwa duga-duganka.
Idan zaka sake alwala bayan fitsari ko ba-haya ko hutu ba sai ka cire safar ba. Zaka iya yin shafa akanta. Amam idan janabah ce ta sameka sai ka cireta yayin wanka.
Don Qarin bayani aduba babul mas'hi alal Khuffi acikin wadannan litattafan :
- ALFIQHU ALAL MAZAHIBIL ARBA'AH.
- ALFIQHUS SUNNAH.
- ALMUGHNEE (NA IBNU QUDAMAH).

WALLAHU A'ALAM

Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕
Post a Comment (0)