HUKUNCIN YIN TAYMAMA A LOKACIN SANYI
https://chat.whatsapp.com/IQUc0RxgCwA3JFiEKl8j5E
*TAMBAYA*❓
Assalamu alaikum Malam shin ya halatta ayi taimama saboda sanyi kuma gashi mutum yana da janaba A jikin shi Saboda mun makara idan muka tsaya dafa ruwan zafi lokaci zai wuce kuma idan nayi amfani da ruwan sanyi zan sani rashin lafiya Saboda ina da lalura ta asthma, ko waje na fita na shaki sanyi sai ciwon ya tashi.
Don Haka na samu kasa mai tsarki nayi amfani da ita, Amma da zarar hantsi ya fito nake yin wankan tsarki
*AMSA*👇
Wa'alaikumus-Salam. Hakika duk wanda Ya tashi yin Sallah kuma yana dauke da Janaba to dole ne sai ya tsarkaka sannan zai yi sallah, Saboda a Cikin Al-qur'ani Allah (Swt) Yana Cewa; "IDAN KUN KASANCE MASU JANABA, TO KUYI TSARKI (Gabanin kuyi Sallah). (Suratul Ma'Ida aya ta 6).
Sai dai kuma Idan Mutum ya kasance a halin tafiya bai samu ruwa ba ko kuma akwai ruwan Idan ya tabasu zasu kawo masa cikas ga Lafiyarsa to Sai yayi taimama kamar yadda Allah bayyana adai cikin al-qur'ani mai girma.
Allah (Swt) yana Cewa, "KUMA IDAN KUN KASANCE MAJINYATA, KO KUWA AKAN TAFIYA, KO DAYA DAGA GAREKU YAZO DAGA KASHI, KO KUKA YI SHAFAYYAR JUNA DA MATA, SA'ANNAN BAKU SAMI RUWA BA TO KUYI NUFIN WURI MAI KYAU (Ma'ana Kuyi taimama)." (Suratul Ma'Ida Aya ta 6).
An ruwaito hadisi daga Amr ibn al-Aas (rta) Yace, "Na gamu da matsalar yin Mafarki (kuma har nayi Inzali) a wani dare da ake yin masifar Sanyi kuma a karshen dare, sannan ina jin tsoro akan cewa, idan nayi wankan tsarki zan mutu, saboda haka sai nayi taimama na gabatar da sallar asuba tare da Abokanan tafiyata.
Suka gayawa Annabi (Saww) abinda ya faru, Sai Ya tambayeni shin ko nayi abinda abokan tafiya ta suka fadi game da Ni a cikin Janaba? Sai na gaya masa abinda ya same ni da dalilina na rashin yin tsarki. Sai na karanta masa fadin Allah (swt), "KUMA KADA KU KASHE KANKU. LALLE NE ALLAH YA KASANCE GAME DAKU MAI JINKAI NE." (Suratul Nisa'I aya 29).
Bayan na kammala sai Annabi (Saww) yayi murmushi baice komai ba. (Imamu Abu Dawood ne, ya ruwsito shi a hadisi na 334; a cikin saheeh Albaani ya kawo shi a cikin Saheeh Abi Dawood.)
Ibn Hajar (Allah ya jikansa) YaCe; "Wannan Hadisi ya yardewa wanda ke tunanin yin Amfani da ruwa zai kashe shi yin taimama, ko saboda Sanyin ruwan ko kuma wani dalili daban, kuma a cikin sa akwai yardewa mutum yayi taimama yayi sallah ga wanda baya iya yin alwala." (A duba a cikin Fatul Baar, 1/454).
Shi kuwa Shaykh ‘Abdul Azeez ibn Baaz (Allah ya jikansa) Cewa yayi, "Idan Har baka iya Daura ruwa ko kuma baka iya saye a makwaftanka a wani wuri zaka iya yin taimama Saboda Allah (Swt) Yace; "SAI KU BI ALLAH DA TAQAWA GWARGWADON ABINDA KUKA SAMI IKON" (Sura Taghaabun aya ta 16) . (A duba a Majmoo’ Fataawa na Ibn Baaz, 10/199,200)
Saboda haka ya halatta Kiyi taimama Idan har babu yanda zaki sami Ruwan dimi
Wallahu A'alam.
Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕