HUKUNCIN ZAMA DA MIJI MAZINACI


*HUKUNCIN ZAMA DA MIJI MAZINACI*

https://chat.whatsapp.com/J1hm5Tw12uYBqfaiPwf28l

*TAMBAYA*❓

Assalamu alaikum warahmatullah , mallam menene hukuncin xama da miji mazinaci ?

*AMSA*👇

Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu

Dafarko dai yana dakyu mu nisanci zargi da munana zato a tsakaninmu da abokanan zamanmu
Allah madaukakin sarki ya hanemu da munana zato a cikin Suratul Hujurat, Ayah 12 Allah yana cewa: YAKU WADANDA SUKE YIIMANI KU NISANCI ABU MAI YAWA NA ZATO LALLAI SASHEN ZATO LAIFI NE ......
HAKANAN ANNABI ( ﷺ ) YACE MU NISANCI ZATO DOMIN SHI ZATO MAFI SHIRYAYYAN ZANCE NE NA KARYA .
Sabida haka Allah da manzon sa sun hana mu mummunan zato bai dace mu dinga zargin juna da aikata sabon Allah ba .
Amma idan mace ta tabbatar Mijinta Yana da dabi'ar ZINA to Abu na farko da zatayi shine tayi masa Nasiha da wa'azi lallai yaji tsron Allah Idan yaki ji to sai ta sanar da magabatanta halin da ake ciki suma sai su same shi suyi masa wa'azi kuma su fadakar dashi hatsarin wannan dabi'ar idan ya tuba ya dena to shikenan sai su cigaba da zaman su Idan kuma yaki denawa to kawai ta nemi ya saketa idan tayi hakan batayi laifi ba domin dabi'ar ZINA tana daya daga cikin dalilan da mace zata iya neman saki idan yaki sakinta to magabatanta sai suyi masa umarni daya saketa idan yaki sakinta sai sukai kararsa wajen al'kali domin ya saketa sabida be halatta Mace ta zauna da MAZINACI BA.
Allah Ya shiryar damu hanya madaidaiciya yasa mudace
wallahu a'alam
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ , ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ

Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕
Post a Comment (0)