*TAMBAYA*❓
Assalamu alaikum
Malam batun matsala nane da maigida na na bude WhatsApp da sabon number Ina yin chat dashi amatsayin wata budurwa, shine yabani labarin kanshi wai yanada mata da yara biyu Amma sun rabu, hankalina yatashi Ina ga kamar auren mu ya mutu duk da cewa Ni da daya muka Haifa dashi sai dai akwai matar da suka rabu da ita wacce suka haifi Yaya biyu.
Dan Allah malam a bincika min ya matsayin aurenmu yake.
*AMSA*👇
Gaskiya Baki Kyauta ba. Wannan Shine Abinda Manzon Allah saw ya hana. Wato bin Diddigin Mutum. Bibiyarsa har sai ka kama shi da Lefi.
Manzon Allah saw Yace DUK WANDA YA KE BIBIYAR WANI AKAN SAI YA GANO LEFINSA. TO SHIMA ALLAH ZAI BI DIDDIGINSA HAR SAI YA KAMA SHI DA ABINDA YAKE AIKATAWA.
Kinga kenan idan Allah ya bi diddiginki. Ba zaki kai Labari ba. Kuma kin sani kamun Allah mai Tsanani ne.
Sannan kuma idan har Allah ya tona Asirinki. Wallahi sai ya tona dukkan Lefin da kike Aikatawa kowa ya Sani.
Sabida haka Ki dena yi gaskiya akan Mijinki ko Kishiyar ki ko makociyarki ko akan wani daban.
Sannan Kuma yin hakan Me ya Kara Miki?
Mata Ku dena Daukar Wayar Miji. Wannan Al'amarin yana kashe Aure Sosai ma kuwa.
Maganar Aure kuma Auren ku yana nan. Me ya same shi? Ba Abinda ya Sami Aurenki.
https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfqds
Allah shine Masani.
Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕