JINKIRTA SALLAMA BAYAN LIMAN KUSKURE NE


اَلسَلامُ عَلَيْكُم وَرَحْمَةُ اَللهِ وَبَرَكاتُهُ‎
Daga Zauren 
   *📌Albahral Ilmu🌴*


*JINKIRTA SALLAMA BAYAN LIMAN, KUSKURE NE!*


*TAMBAYA*❓

Salamun alaykum barka da safiya mallam. Mutum ne Yana bin imam sallah sai imam ya sallame shikuma sai ya qara kusan mintuna biyar kamun ya sallame. Shin yin hakan sunnah ne.

*AMSA*👇

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuh. Alhamdu lillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu ala rasulillah wa ala alihi wa sahbihi ajma'in.

Wannan ba Sunnah bane, ta'addanci ne da rashin biyayya ga liman. Wannan mamu bai yi aiki da umarnin Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama gare mu na cewa, an saka mana liman ne don muyi koyi da shi ne, shi kuwa koyi baya ɗaukar jinkiri.

2358 - 1057 - «إنما جعل الإمام ليؤتم به فإذا كبر فكبروا وإذا قرأ فأنصتوا وإذا قال سمع الله لمن حمده فقولوا: ربنا لك الحمد» .
(صحيح) ... [ن] عن أبي هريرة. الإرواء 332، 394.

Bayan wannan zance sai mamu suka rabu gida biyu, da masu wuce gona da iri, masu zurfafawa, irin wannan mutum ke nan, da kuma aiki tare da liman, dukkan su basu dace da aiki da hadisin ba. Wanda ya dace shine mai biyayya da zaran liman ya gama aiki, ba tare da jinkiri ko gaugawa ba. 

Mai koyi na aikata abin da mai koyar da shi ne, da ya gama, ba tare da wani jinkiri ba. 

Wallahu ta'aala a'lam.

 *_Amsawa_* :

 *Malam Aliyu Abubakar Masanawa*
Post a Comment (0)