HUKUNCIN SAKI A CIKIN HAILA



اَلسَلامُ عَلَيْكُم وَرَحْمَةُ اَللهِ وَبَرَكاتُهُ‎

Daga Zauren
    📌 *Albahral Ilmu*🌴

✍🏻Rubutawa
     Abdulkadeer Umar Alshinkafawy.


*HUKUNCIN SAKI A CIKIN HAILA:* 


*TAMBAYA*❓

 _As-Salaam Alaikum._ 

Don Allaah menene hukuncin matar da aka sake ta alhali tana jini? 

 *AMSA*👇

 _Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh._ 

Malamai sun kasa saki gida biyu ne: Akwai sakin Sunnah akwai sakin bidi’a.

Sakin Bidi’ah: Shi ne ɗayan waɗannan:

(i) Sakin da ya auku a cikin haila ko nifasi.

(ii) Ko wanda ya auku a cikin tsarkin da ya riga ya sadu da ita a cikinsa.

(iii) Ko kuma ya aukar da saki fiye da ɗaya a lokaci guda, kamar ya ce: *Na sake ki saki uku!* Ko kuma ya ce: *Na sake ki! Na sake ki!! Na sake ki!!!* 

Game da hukuncin saki a cikin haila malamai sun sha bamban. 

Amma abin da ya fi daidai shi ne: Aukuwarsa a matsayin saki guda, wanda kuma akwai kome a cikinsa, saboda hadisin Ibn Umar _(Radiyal Laahu Anhumaa)_ wanda ya saki matarsa a cikin haila. Da maganar ta kai ga Annabi _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ sai ya ce:
 
مُرْهُ فَلْيُرَاجِعْهَا ثُمَّ يُمْسِكْهَا حَتَّى تَطْهُرَ ، ثُمَّ تَحِيضُ ثُمَّ تَطْهُرُ ، فَإِنْ شَاءَ أَمْسَكَ بَعْدُ ، وَإِنْ شَاءَ طَلَّقَ قَبْلَ أَنْ يَمَسَّ ، تِلْكَ هِيَ الْعِدَّةُ الَّتِي أَمَرَ اللهُ أَنْ تُطَلَّقَ لَهَا النِّسَاءُ
Ka umurce shi ya mayar da ita, ya zauna da ita har sai ta yi tsarki, sannan ta sake yin haila kuma ta sake yin tsarki. To, daga nan in ya so sai ya cigaba da zama da ita, in kuma ya so sai ya sake ta tun kafin ya sadu da ita. Wannan ce iddar da Allaah ya yi umurni a saki mata a halin suna fuskantar ta _. Sahih Al-Bukhaariy: 5251, Sahih Muslim: 1471._ 

Don haka, ana neman mijin da ya yi hakan ya ɗauki waɗannan matakan:

(i) Ya tuba ga Allaah Ta’aala saboda wannan laifin na bidi’a da ya yi.

(ii) Ya komo da ita ɗakinta, har sai ta kammala wannan hailar.

(iii) Har sai ta sake yin wata hailar, kuma sai ta tsarkaka daga wannan hailar.

(iv) Daga nan yana iya sakin ta na-biyu tun kafin ya sadu da ita, in ya yi buƙata.

(v) Ko kuma ya cigaba da zama da ita da ragowar igiya biyu.

Allaah ya shiryar da mu.

 _Wal Laahu A’lam._ 

Ansaw:

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy
Post a Comment (0)