MA'ANAR AZUMI DA FALALARSA


*MAKARANTAR AZUMI [001]* 

📌 ```MA’ANAR AZUMI DA FALALAR SA``` 

1-   Azumi: shine kamewa daga barin duk abubuwan da suke karya Azumi, tun daga bullowar Al-fijir har zuwa faɗuwar Rana, amma tare da Niyya ta Ibadah.

2-   Allah Ya ambata mana a cikin Al-Qur’ani cewa yin azumi shi yafi alheri garemu saboda darajar sa.

3-   Ya ishi azumi falala da daraja da har Allah SWT Ya jingina mai azumin da cewa nashi ne, Allah bai fadi keke-da-keken ladan ba, Allah ne kadai yasan tarin ladar da ya tanadar ma bawan sa da yake Azumi, kamar yadda ya tabbata a Hadisi ingantacce daga Sahabi Abu Hurairah.

4-   Allah Ya kebance masu azumi da samun wata kofa a Aljannah wacce babu wasu wadanda zasu samu damar shiga ta wannan kofar sai su kadai,

5-   Azumi Garkuwa ne musamman ga wanda sha’awa ta tsanantu gare shi, haka kuma garkuwa ne, tsari ne daga shiga Wuta.

6-   Haka kuma shi Azumi yana raba Zukata daga Sha’awa, yana raba su da miyagun ɗabi’un da suka zamar musu jiki, sai su wayi-gari suna masu natsuwa da kwanciyar hankali, To idan ka fahimci cewa Azumi yana takure sha’awa yana tursasa ta, alhali kuwa itace take shashantar da Mutum kuma take kusantar dashi ga Wuta, kaga kenan Azumi ya zama katangar Ƙarfe tsakanin Mutum da Wuta.

7-   A cikin Hadisi ingantacce daga Sahabi Abu Sa’eed Al-khudriy, Manzon Allah SAW Ya ce: “Babu wani Bawa da zai azumci wani yini saboda Allah, sai Allah Ya nesanta fuskar shi daga Wuta saboda wannan azumin tsawon Shekaru Saba’in”.

8-   Sunnar Annabi ingantacciya tazo a wurare masu yawa sun nuna falalar da Azumi yake dashi.

Allah Ya azurta mu da samun wadannan faloli, Ya kuma bamu Ladan wannan Azumi, ya biya mana bukatocin mu Ya ye mana halin da muke ciki, Amin.

*Twitter* 👇🏿
https://twitter.com/AnnasihaTv?s=09

*Telegram* 👇🏾
https://t.me/AnnasihaTvChannel
Post a Comment (0)