MAGANIN MATSALAR MIYAGUN MAFARKAI


*MAGANIN MATSALAR MIYAGUN MAFARKAI :*

https://chat.whatsapp.com/IQUc0RxgCwA3JFiEKl8j5E

*TAMBAYA*❓

Assalamu Alaika Allah gafarta malam. Na kasance ina mafarki da macizai ko da yaushe suna bina wani lokaci ma har su cije ni. Malam wannan mafarkin zan iya cewa tun ban mallaki hankali na sosai ba nake yinsu yanxu har Allah yayi nayi aure amma ban daina ba. Ina kokarin yin adduoi kafin nayi bacci amma hakan baya hana faruwar mafarkin. Naji ana ce mafarki da macizai alamar kana da aljanu ne ki makiya ni kuma bana jin alamar aljanu a jikina. Mal na rasa yadda zanyi don Allah a taimakeni da wasu adduoi na musamman ko kuma magani. Nagode. Daga wata baiwar Allah.

*AMSA*👇

Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Duk da kin bayyana cewar ba kya ganin wasu manyan alamomin shafar Aljanu tare dake, ina dai baki shawarar cewa ki duba wani posting (rubutu) da muka wallafa anan Zauren Fiqhu mai taken "Alamomin shafar Aljanu" ki karantashi tun daga farko har karshe watakil ba za'a rasa wasu alamomin da kike ji ba.
Kuma ba wai sai mutum ya fa'di Qasa yana ihu shine ka'dai alamar shafar Aljanu ba. Daga cikin manyan alamomin akwai yawan faduwar gaba, ciwon kai, rikicewar tunani, yawan fushi, rashin damuwa da ibadah, yawan tunani marassa kyau, kokwanto acikkn ibadah, etc.
Ki nemi man habba da na Zaitun ki hadasu waje guda sannan ki tofa wadannan surorin aciki : suratul baqarah, yaseen, Zukhruf, Qamar, Mulk, buruj, Feel, Quraish, Ikhlas, falaq da nas duk acikinsa.
Daga nan sai ki rika shafawa duk jikinki kafin ki kwanta barci. Sannan da rana ma ki sake shafawa. Kuma ki rika shan cokali guda da safe, da yamma ma haka.
Zaki ci gaba da yin haka har tsawon watanni biyu ko uku , kuma atsawon wannan lokacin ki rika karanta koda hizifi biyu na Alqur'ani a kullum, Kuma kina sauraron Qira'ar karatun Alqur'ani na tsawon awa guda ko biyu.
Ki lazimci dukkan zikirai na safe da yamma, da kuma La haula wala Quwwata illa billahil Aliyyil Azeem sau 100 safe da yamma, da kuma Hasbunallahu wa ni'imal wakeel shima haka.
In sha Allahu kowanne irin shaidani ne dolensa yabar jikinki. Kuma koda matsalar sihiri ce ko kambun ido zaki warke in sha Allahu.
Idan kuma kina bukatar wasu magunguna ko shawarwari bayan wannan, to ki tuntubi Zauren Fiqhu akan wadannan lambobin 07064213990 08163621213.
WALLAHU A'ALAM.

Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕
Post a Comment (0)