TONON ASIRIN GIDAN AURE


*TONA ASIRIN GIDAN AURE:* 

https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfqds

*TAMBAYA*❓

As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah.

Menene hukuncin ma’aurata su riƙa faɗin sirrinsu a cikin group na social media?

 *AMSA*👇 

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

Ƙullin aure a musulunci ƙulli ne mai ƙarfi ƙwarai da gaske, kamar yadda Allaah ya faɗa:

 وَكَیۡفَ تَأۡخُذُونَهُۥ وَقَدۡ أَفۡضَىٰ بَعۡضُكُمۡ إِلَىٰ بَعۡضࣲ وَأَخَذۡنَ مِنكُم مِّیثَـٰقًا غَلِیظࣰا
Kuma ta yaya za ku karɓe shi (watau sadakin da kuka ba matanku), alhali kuwa sashenku ya sadu da sashe, kuma sun riƙi alƙawari mai ƙarfi daga wurinku. (Surah An-Nisaa’: 21)

Kamar kuma yadda ya ambaci irin wannan alƙawarin game da manyan Annabawansa: Ulul-Azmi Minar Rusul:

 وَإِذۡ أَخَذۡنَا مِنَ ٱلنَّبِیِّـۧنَ مِیثَـٰقَهُمۡ وَمِنكَ وَمِن نُّوحࣲ وَإِبۡرَ ٰ⁠هِیمَ وَمُوسَىٰ وَعِیسَى ٱبۡنِ مَرۡیَمَۖ وَأَخَذۡنَا مِنۡهُم مِّیثَـٰقًا غَلِیظࣰا
Kuma ka tuna lokacin da muka riƙi alƙawarin Annabawa, kuma daga gare ka, kuma daga Nuuh da Ibrahim da Musa da Isaa Bn Maryam, kuma mun riƙi alƙawari mai ƙarfi daga gare su. (Surah Al-Ahzaab: 7).

Bayan an ɗaura aure a tsakanin ma’aurata kamata ya yi su zama abu guda, masoya kuma mataimaka juna. Kuma bai kamata su bari a riƙa jin tsakaninsu ba.  

Hanyoyin warware matsalolin da kan taso lokaci bayan lokaci a tsakanin ma’aurata sanannu ne a cikin Al-Kitaab Was Sunnah a wurin malamai.

Daga cikin hanyoyin korewa da maganin matsalolin a dunƙule kuma a taƙaice akwai:

(i) Su riƙa yi wa maganganu da ayyukan junansu kyakkyawar fassara, tare da neman fassara da ƙarin bayani a kan duk abin da ya shige duhu na wannan ɗin.

(ii) Su riƙa zama suna tattauna matsalolin da ya shafe su ko ya shafi ɗayansu, maimakon fitar da matsalar zuwa waje.

(iii) Su mayar da matsalar da suka kasa warwarewa ga malami ko limamin unguwarsu ko wanda ya ɗaura musu auren, shi ya fi da su kai maganar ga iyayensu.

Domin malami yana da ƙarin masaniya game da Ayoyi da Hadisai da maganganun malamai a bayan gogewa a kan al’amuran rayuwa da zamantakewar jama’a na zamanin baya da wannan zamani.

Yawanci idan matsalar ma’aurata ta kai ga iyayensu, sukan samu damuwa da tashin hankali sosai, kuma sukan daɗe ba su manta ba ko da kuwa su ma’auratan sun daɗe da yin sulhu a tsakaninsu.

Abu ne sananne cewa: Shafukan tashoshin sada zumunta da na’urorin wayoyin tafi-da-gidanka ba wurare ne na sakin bayani ko ajiyewa balle ma adanawa ko ɓoye sirri ba. Shi kuwa musulmi yawancin al’amuransa in ma ba duk ba suna buƙatar sirri, don tsare mutuncinsa da martabarsa.

Amma duk wanda ya shigar da wani rubutu ko wata magana ko hoto a cikin irin waɗannan shafukan na sada zumunta ko wayoyin hannu, to kuwa suna nan har abada kuma ko kusa ba ɓoyayyu ba ne.

Don haka, ba wai ’ya’ya da jikokin ma’auratan da suka saka maganar ba, har tattaɓa-kunnensu ma za su zo su ga wannan abin, matuƙar dai sun yi bincike a kan wannan shafin.

Don haka, dai wajibi ne mutane su san irin abin da za su saka a cikin kowane irin group na social media, domin ko ba komai akwai tambayoyi da za su biyo baya a kan hakan a gaban Ubangijin Halittu a ranar Lahira.

Allaah ya shiryar da mu.

Wal Laahu A’lam.

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕
Post a Comment (0)