*_▪️📚 MANUFOFIN SHARI'AR MUSULUNCI 11 📚▪️_*
*_ME YA SA AKA HANA YIN ƘARI AKAN MATA HUƊU?_*
*_✍️ Yusuf Lawal Yusuf_*
Allah Ya halattawa musulmi auran mata huɗu kamar yadda Allah ya bayyana hakan a Suratun Nisa'i, aya ta (3). Sai dai haramun ne ya auri matan da suka zarce haka, saboda lokacin da Gailan ɗan Salama ya musulunta, yana da mata goma m, Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya umarci shi ya saki guda shida ya bar huɗu kawai, kamar yadda Tirmizi ya rawaito. Akwai hikimomi da suka sanya aka hana ƙari akan mata huɗu:
1. Nuna darajar aure da kuma ƙimanta shi.
2. In mutum ya auri zama da mata huɗu zai iya ɗorawa kansa nauyin da ba zai iya ɗauka ba.
3. Zai iya shigar da matan cikin zina, saboda akwai yiwuwar ba zai iya biya musu buƙata yadda ya kamata ba.
Duba: Tafsirul Ƙur'anil Azhim na Ibnu Kathir, 2/188 da kuma Addurrah Almukhtasarah, shafi na 319.
Tsakure daga cikin littafin Manufofin Shari'ar Musulunci, wallafar Sheikh Dr. Jamilu Yusuf Zarewa.
*_12th Rajab, 1442A.H (24/02/2021)_*