﷽
اَلسَلامُ عَلَيْكُم وَرَحْمَةُ اَللهِ وَبَرَكاتُهُ
Daga Zauren
📌 *Albaharal Ilmu*🌴
✍🏻Rubutawa
Abdulkadeer Umar Alshinkafawy.
*SHIN MACE ZATA IYA JAGORANTAR YAN'UWANTA MATA A SALLAH*
*TAMBAYA*❓
Shin Ya halatta mace tayi Limanci abisa 'Yan uwanta Mata? ko kuwa be halatta ba?
(daga Khadijah Abdullahi)
*AMSA*👇
Gaskiya akwai maganganu mabambanta akan wannan Mas'alar.
Imam Abu Haneefa yace Makruhi ne mace tayi limanci ga 'Yan uwanta mata. yayin da Imam Ahmad da Imamush-Shafi'iy: Suka ce ya halatta.
Shi kuma Imamu Malik yace bai Halatta ba.Kuma kowannensu yana da tasa madogarar.
Su wadancan Shugabanni guda uku na farko sun dogara ne da Hadisin nan na Sayyidah Ummu Waraqah (rta).
Wacce ta kasance daga cikin mataye masu ilimi daga cikin Ansaar (mutanen Madinah). Ta nemi Izinin Manzon Allah (saww) cewar zata bishi wajen Yaki domin samun shahadah. sai yace mata A'a. ki zauna agidanki. Allah zai azurtaki da samun shahada.
Daga baya sai ta sake neman Izininsa akan ta rika jagorantar mutanen gidanta a Sallah, Kuma ya amince mata (Saboda mahaddaciyar Al_Qur'ani ce). harma ya sanya mata wani Tsoho ya rika yi mata Ladanci.
(Wannan Sahihin Hadithi ne. aduba Sunanu Abu-Dawud, hadisi na 592. da kuma Ibnu Khuzaymah Hadisi na 1676).
Sannan Akwai wani hadisin Sayyidah A'ishah da Sayyidah Ummu Salamah (rta) wanda yazo acikin ALMUSANNAF na Imam Abdurrazaq (malamin Imamu Ahamad bn Hanbal ne). ya kawo hadisin alamba ta 5086.
Da kuma Daraqutny (Malamin Imammun Nisa'iy) ya ruwaito hadisin littafinsa (Sunanu) Juzu'i na 1 shafi na 404.
Da kuma Bayhaqy, Juzu'i na 3 shafi na 131.
Dukkansu sun ruwaito daga Abu Hazim (Maisarah bn habeeb, thiqah ne kuma babban Malamin Jur'hu wat-ta'adeel) shi kuma daga Ra'itatul_Hanaf
iyya, ita kuma daga A'ishah (@ummul mumineen).
"Sayyidah A'ishah ta kasance tana jagorantarsu aSallar farillah, amma tana tsayawa ne acikin Sahun,"
Ibnu Aby shaybah da Imamul Hakim suma sun ruwaito cewar Ita kanta Sayyidah A'ishah ita take yin kiran Sallar da Iqamah.
(aduba cikin musnad nasa
juzu'i na 2 shafi na 89).
Shafi'iy ya ruwaito da kuma Abdurrazaq (hadisi na 5082) cewar:
"Ummu Salamah ta kasance tana Limancinmu (mata) asallah. kuma tana tsayawa ne acikinmu a sahun farko).
Akwai kuma ruwayar Ikramah daga Ibnu Abbas (ra) yana cewa : MACE ZATA IYA JAGORANTAR 'YAN UWANTA MATA ASALLAH, ALHALI TANA TSAYE ATSAKANINSU".
(Aduba ALMUSANNAF hadisi mai lamba 5083)..
SHIN YA HALATTA MACE TAYI LIMANCIN MAZA ? KO KUMA MAZA DA MATA AHADE??
A'A WANNAN BAI HALATTA BA.. ABISA ITTIFAQIN DUKKAN MAZHABOBI.
Duk wanda ya halatta hakan awannan zamanin yayi ne abisa SON ZUCIYA. Domin kuwa basu da wata Qakkarfar hujjah.
Wancan Hadisin ma na Ummu waraqah, malamai sunce ya takaitu ne abisa mutanen gidanta kadai.. wani tsoho ne da kuma bawanta da kuyangarta.
Imamut Tabary da Abuth-thaur da Al_Mazany sun tafi abisa ingancin yin hakan. sa'banin Dukkan Ijma'in sauran Malamai da Mazhabobi.
SHIN YA HALATTA NAMIJI GUDA DAYA YA LIMANCI JAMA'AR MATA?
EH YA HALATTA. Idan matansa ne ko muharramansa. SABODA HADISIN NAN NA UBAYYU BN KA'AB. yayi limancin wasu matan gidansa. sai yazo ya tambayi Manzo (as). Amma bai hana shi ba.
SHIN WAJIBI NE MATA SUYI SALLAH AJAM'I?
A'A bawajibi bane. mubahi ne, kamar yadda maluma suka fada.
Domin kuwa Sallar mace ita kadai acikin dakin Mijinta shine yafi Lada fiye da fito tabi jam'i koda kuma abayan wanne malami ne. kuma koda acikin Masallacin harami ne.
(Don Qarin bayani aduba ALMUGHNY littafin Ibnu Qudamah, Juzu'i na 2 shafi na 202
Da kuma ALMUHAZZAB juzu'i na 4 shafi na 295.
Da kuma JAMI'U AHKAMIN NISA'I Juzu'i na 1 shafi na 351
Wannan shine dan abinda ya sawwaka.
wallahu a'alam.
Ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar SHARING, wasu da yawa zasu amfana.
Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
07064746551
*_Group Admin: ▽_*
*Abdulkadeer Umar Alshnkafawy*