NEMAN SAKI DON RASHIN HAIHUWA


*NEMAN SAKI DON RASHIN HAIHUWA:*

https://chat.whatsapp.com/IZhc4HXjGXFDOuOmx3ceZA

*TAMBAYA*❓

As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah.
Ko ta halatta mace ta nemi saki bayan sun tafi asibiti an tabbatar musu cewa ƙwayayen mijin ba za su iya haihuwa ba?


*AMSA*👇

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.
[1] Ya halatta mace ta nemi miji ya sake ta matuƙar dai akwai larura ko damuwa kwatankwacin irin wannan, kamar yadda Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:
Duk matar da ta nemi saki daga mijinta ba da wani dalili ba, to kuwa ko ƙanshin Aljannah ba za ta ji ba.
Wannan ya nuna: Idan da dalili ne to, wannan ba zai hana ta shiga Aljannah ba, in shaa’al Laah. Wal Laahu A’lam.
Amma duk da haka, abu ne mai kyau mace ta san cewa: Ita haihuwa kyauta ko baiwa ce daga Allaah Ubangijin Halittu, yana bayar da ita ga wanda ya ga dama, kuma ya hana ta ga wanda ya ga dama, domin wata hikima ta sa:
Na Allaah ne duk abin da ke cikin Sammai da Ƙasa. Yana halitta abin da ya so. Yana yin baiwar ’ya’ya mata ga wanda ya so; kuma yana yin baiwar ’ya’ya maza ga wanda ya so. Ko ya gauraya su maza da mata. Kuma yana barin wanda ya so a matsayin bakarare (mara haihuwa). Haƙiƙa! Shi Masani ne, Mai Iko.
Tun dayake Shi Mai Cikakken Iko ne a kan dukkan komai, ashe zai iya sauya halin rashin haihuwa da miji ko mata ke fama da shi zuwa ga halin samun haihuwa, kamar yadda ya auku ga manyan Annabawansa: Ibrahim da Zakariyya (Alaihimas Salaatu Was Salaam). A tarihi kuma ba mu ji cewa matan aurensu sun nemi saki saboda hakan ba!
Don haka dai, abin da ya fi kyau a nan sai mu yi ƙan-ƙan da kai gare shi (Subhaanahu Wa Ta’aala), mu yi yawaita yin addu’a da roƙo gare shi, da fatan Allaah ya kawo waraka ga irin waɗannan ma’auratan, kuma ya ba su na-gari daga cikin falalarsa.
Sannan kuma lallai ne mu san cewa a yau muna rayuwa ne a cikin wani zamani da maƙiya musulmi da musulunci suka yawaita, kuma suke cin karensu ba babbaka. Muna ji da ganin yadda ake ta ƙulla wa jama’ar duniya – musamman marasa ƙarfi - makirci da kutungwila iri-iri. Daga ciki akwai mummunan makircin da wasu turawa masu ƙarfi arziki suke yin shigar burtu, suna nuna cewa su mataimaka talakawa ne da mata da yara da sauran raunana marasa galihu, wai su masu bayar da taimako da gudunmawa ce gare su a ƙasashe masu tasowa! Alhali kuwa a ƙarƙashin ƙasa su mugayen azzalumai ne masu aiwatar da munanan ayyukan ta’addanci a cikin al’umma. Binciken da masana suka gudanar ya nuna cewa:
Ta amfani da ayyukan bayar da agaji ko riga-kafi ne suke samun daman kutsawa a cikin ƙauyuka da biranenmu, har su iya shigar da sinadarai masu hatsari ga lafiyar jama’a tun suna ƙanana.
Ta amfani da wannan hanyar ce dai suke iya shigar da manyan makamai da mugayen makisa ’yan ta’adda a cikin al’ummarmu a cikin birane da ƙauyuka.
Saboda samun amincewar da shugabanni suka yi da su a cikin ƙasashe irin namu ne har suke iya amfani da maƙudan kuɗaɗen da ko haraji ba a cire musu, kuma suke taimakawa wurin cigaba da ɗaure wa ta’addanci gindi da ƙarfafa shi a sassa da yawa na duniya.
Ta hanyar ta’addancin ne suke iya ƙona garuwa da ƙauyuka su tarwatsa al’umma, da manufar su watse su rabu da irin shuka masu albarka da suka gada daga iyaye da kakanninsu.
Wannan hanyar ita ta ke ba su daman shigar da irin shukan da suka kirkira a ɗakunansu na bincike da gwaje-gwaje a cikin al’umma, ta hanyar bayar da taimako ko gudunmawa ga waɗanda suka samu ikon komawa garuruwansu bayan gama rikice-rikicen.
Abincin da aka samu daga cikin irin wannan irin shukan shi ke zama sanadin lalata ƙwayayen haihuwar mazaje da yawa a cikin irin waɗannan ƙasashen, ta yadda ba za su iya haihuwa ba.
Wannan kuma shi zai sa matan aurensu su buƙatu ga neman a yi musu artificial insemination, watau a haɗa ƙwayayensu da na wasu mazan a asibitocinsu don neman haihuwa.
Ta wannan hanyar ce masu binciken suka gano cewa likitocin za su samu daman ɗebe irin ƙwayayen haihuwar da suka so daga matan, domin yin amfani da su daga baya a wurin ƙera sassan jikkunan mutane!
Allaah ya kiyaye.
Don haka, wajibi a kan hukumomi da dukkan jama’a shi ne: Su tashi tsaye su yaƙi wannan matsalar ta ta’addanci a cikin ƙasa da maƙwabtanta. Kuma su yi taka-tsantsan game da irin shukan da ake shigo mana da su daga ƙasashen ƙetare. Sannan dole mu san wane likita ne, kuma a wane asibiti ne za mu kai matanmu domin yin awo da sauran al’amuran da suka shafi haihuwarsu.
Sannan kuma ya kamata ma’aurata su bi a hankali, kar su yi gaggawa wurin neman saki saboda larurar rashin haihuwa kaɗai, domin ba lallai ya zama hakan daga tsarin halittan ma’auratan ba ne, daga makircin makirai ne! Musamman ma dayake suna iya samun ’ya’yan riƙo daga wurin ’yan uwa da dangi ko daga gidajen marayu a ko’ina.
Allaah ya shiryar da mu, ya kare mu daga dukkan makircin makirai, ya karya ƙarfinsu, ya ruguza mugun nufinsu, ya mayar musu da makircinsu damugun ƙullinsu cikin kawunansu da magoya-bayansu.

Wal Laahu A’lam.

Sheikh Muhammad Abdullah Assalafiy

‎Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
 *_Group Admin: 👇_*
 *MAL. HAMISU IBN YUSUF*
Post a Comment (0)