HUKUNCIN KWANAN ƘAWAYE A GIDAN AMARYA


*HUKUNCIN KWANAN KAWAYE A GIDAN AMARYA*

https://chat.whatsapp.com/LRPQDrs7qSoKXuSspoPkFm

*TAMBAYA*❓

Assalamu Alaikum Wa Rahmatullah, Sabahul Khair, Ya Mu'allim, Ina tambaya, menene hukuncin kwana da kawayen amarya ke yi a ranar da aka daura mana Aure a gidan mijinta? Nagode.


*AMSA*👇

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuh. Alhamdu lillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu ala rasulillah wa ala alihi wa sahbihi ajma'in.

Halasci ko haramcin kwanan ƙawaye a gidan amarya, ya danganta da yanayi da lokaci ne. 

Yana halatta ne idan akwai tabbacin kuɓutar wacce zata kwana daga lalata da lalacewar tarbiyya ne. Sannan sai idan za'a amintu daga cakuɗuwar maza (abokanan ango) ajanabiyyai, da matan, ƙawayen amaryar, zance ko kuma fasikanci a tsakanin su da junan su. Bayan haka sai idan ƙawayen ba zasu cire tufafin su ba a gidan.

Amma duba da abin da yake na al'adar a irin wannan yanayi, kwanan ƙawayen amarya a gidan amarya, a nan ƙasar hausa, babu komai cikin shi sai sharri da lalata, galiban, don haka baya halatta. Dalili kuwa shi ne, a nan ne, wata take fara koyon zina. Akwai kaɗaituwa da kuma cakuɗuwa tsakanin abokanan ango da ƙawayen amarya, wanda hakan bai haramun ne, a nan ne wata ke cikin shege, a nan wata ke zubar da tarbiyar da iyayen ta suka bata. Har ila yau, a nan ne galibi, wata ke tsintar muguwar ƙawa da zata kai ta ga halaka. Wata a nan take sababin kashe ma amaryar auren ta, ta hanyar gina haramtacciyar alaƙa da angon. Sannan wannan haɗuwa galibi, bata rabuwa da cecekuce da zai haifar da rashin jituwa, faɗa da gaba tsakanin ƙawayen amaryar. 

Daga ƙarshe, tambaya ita ce, menene amfanin kwanan ƙawayen a gidan amarya ko kuma wace fa'ida yake haifarwa? Babu wata fa'ida galiban, sai fitsara da kwaɗayin kuɗin maza da sauran ababe na rashin kunya da rashin mutunci. Wannan al'ada ce, irin wacce, ya zamo wajibi kan musulmi su yaƙe ta, sannan iyaye, Mallamai da shuwagabanni su hana ta, domin tana cikin munanan ɗabi'un da ke rusa tarbiyar al'ummar musulmi. 

Wallahu ta'aala a'lam.

 *_Amsawa_* :

 *Malam Aliyu Abubakar Masanawa*

‎Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
 *_Group Admin: 👇_*
 *MAL. HAMISU IBN YUSUF*
Post a Comment (0)