🌙RAMADHAN🌙 //01
"يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا كُتِبَ عَلَيْكُمُ الصِّيَامُ كَمَا كُتِبَ عَلَى الَّذِينَ مِن قَبْلِكُمْ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ". البقرة (183) Al-Baqara
Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! An wajabta azumi a kanku kamar yadda aka wajabta shi a kan waɗanda suke daga gabãninku, tsammãninku, zã ku yi taƙawa
"أَيَّامًا مَّعْدُودَاتٍ ۚ فَمَن كَانَ مِنكُم مَّرِيضًا أَوْ عَلَىٰ سَفَرٍ فَعِدَّةٌ مِّنْ أَيَّامٍ أُخَرَ ۚ وَعَلَى الَّذِينَ يُطِيقُونَهُ فِدْيَةٌ طَعَامُ مِسْكِينٍ ۖ فَمَن تَطَوَّعَ خَيْرًا فَهُوَ خَيْرٌ لَّهُ ۚ وَأَن تَصُومُوا خَيْرٌ لَّكُمْ ۖ إِن كُنتُمْ تَعْلَمُونَ". البقرة (184) Al-Baqara
Kwanuka ƙidãyayyu. To, wanda ya kasance daga gare ku majinyaci ko kuwa yana a kan tafiya, sai (ya biya) adadi daga wasu kwanuka na dabam. Kuma a kan waɗanda suke yin sa da wahala akwai fansa; ciyar da matalauci, sai dai wanda ya ƙãra alhẽri to, shi ne mafi alhẽri a gare shi. Kuma ku yi azumi (da wahalar) ne mafi alhẽri a gare ku idan kun kasance kuna sani.
#Zaurandalibanilimi
TELEGRAM
https://t.me/Zaurandalibanilimi
INSTAGRAM
https://instagram.com/zaurandalibanilimii?igshid=emf6f90ssc24