LABARIN WANI BAWAN ALLAH MAI GODIYA
'Daya daga cikin magabata na kwarai ya bada labari yana cewa:
"Na wuce ta kusa da wani Qauye a Qasar Misra ina kan hanyata ta tafiya wajen Ribadi (wato jiran kan iyakar Musulmai saboda kar kafirai su kawo hari).
Sai na tsinkayi wani bawan Allah yana zaune acikin duhu. Bashi da idanu (wato makaho ne) kuma bashi da hannaye, bashi da Qafafu. Yana fama da dukkan wahalhalu. Amma sai naji yana addu'a yana cewa :
"Godiya ta tabbata agareka Ya Allah, irin godiyar da ta hade dukkan adadin godiyar da dukkan halittunka sukayi maka. Saboda ni'imar da kayi agareni kuma ka fifitani bisa mafiya yawan Halittunka".
Da naji haka mai mamaki ya kamani. Sai nace masa "Yanzu kai, saboda wacce ni'imar kake gode ma Allah? Kuma saboda wacce fifitawar kake gode masa? Domin wallahi babu wani nau'in jinya ko bala'i fache sai da na ganka acikinsa".
Sai yace mun "Shin kaga halin da nake ciki ko? To wallahi da ache Allah zai umurci sammai suyi min ruwan wuta in babbake acikinta, ko kuma ya umurci duwatsun duniyar nan su danneni su ragargazani, sannan ya umurci Koguna su hadiyeni, wallahi babu abinda zanyi fache in Qara gode masa da kuma kirari agareshi".
Sannan yace mun "Don Allah ina da wata bukata agareka. Ina da wata 'diyata wacce take zuwa tana yi mun hidima kuma ina yin buda-bakin azumina tare da ita, (ban ganta ba) ko zaka dubo min inda ta shiga?".
Da naji haka sai nace "In sha Allahu watakil ta dalilin hidimar da zanyi ma wannan waliyyin Allahn, in samu Qarin kusanci da Allah Madaukakin Sarki..
Don haka na fita domin nemanta acikin sahara. sai na tarar dabbobin daji sun cinyeta sunyi kacha-kacha da namanta. Sai nace "Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!!.
Yanzu ta yaya zan iya gaya ma wannan salihin mutum cewar yarinyarsa ta rasu?"
Da na dawo wajensa sai na tambayeshi "Ya kai bawan Allah! Shin kai ne kafi alkhairi awajen Allah, ko kuwa Annabi Ayyuba (as)? Domin shi Allah ya jarabceshi acikin jikinsa da dukiyarsa da 'ya'yansa da iyalansa".
Sai yace mun "A'a Annabi Ayyub (alaihis salam) shine babba, shi yafi alkhairi".
Sai nace masa "To yarinyar da kace in dubo maka, naje na tarar dabbobin daji sun cinyeta".
Da yaji haka sai yace "Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya rabani da duniyar nan ba tare da ya sanya mun Qaunar wani abun cikinta ba".
Daga nan kawai sai naga ya fadi Qasa ya mutu. (SUBHANALLAH).
Da naga haka sai nace "Inna Lillahi wa inna ilaihi raji'un! Yanzu waye zai taimaka mun in wanke wannan gawar sannan in binneta?.
Nan da nan sai naga wasu mutane masu yin ribadi sun taho akan dawakai. Sai nayi musu ishara cewa su tsaya.
Da suka juyo sai na basu labarin dukkan abinda ya faru. Don haka suka tayani muka wankeshi muka sanya masa likkafani sannan muka sallaceshi muka binneshi awannan Kauyen. Sannan wadannan Mazajen suka hau dawakansu suka ci gaba da tafiyarsu.
Ni kuwa na tsaya na kwana awannan Qauyen, na kasa nisantar inda wannan mutumin yake.
Bayan Sulusin dare ya wuce, sai na fara mafarki kamar ina tare da wannan bawan Allahn acikin wani koren lambu, yana sanye da wasu tufafi koraye masu kyau. Yana tsaye yana karatun Alqur'ani (dukkan gabobin jikinsa sun dawo).
Sai nace masa "Shin ba kaine Sahibina na jiya ba?" Sai yace mun "Kwarai kuwa nine".
Sai nace masa "To yaya akayi ka samu irin wannan matsayi haka?".
Sai yace "Hakika ni na samu wani matsayi wanda ba kowanne mai hakuri ne yake samun irinsa ba. Sai dai wadanda suke da hakuri da juriya alokacin tsananin bala'i, Kuma suke da mutukar godiya alokacin yalwa".
Zauren Fiqhu ya dauko wannan Qissar ne daga littafin Sifatus Safwah na Ibnul Jawzee. juzu'i na 2, shafi na 452.
BAYANI
********
Wannan Qissar tana karantar damu abubuwa da yawa. Daga ciki akwai :
- GIRMAMA MUTANE : Kar ka raina mutum don ka ganshi da wata nakasa ajikinsa. Domin zata yiwu ya zarceka wajen tsoron Allah don haka ya fika matsayi awajen Allah..
Lafiya da dukiya da babban matsayin da Allah ya baka, ba wai yana nufin kafi kowa daraja awajensa bane. A'a zata yiwu acikin boyi-boyin da suke maka aikin gidanka, ko masinjojin dake ofishinka, ko cikin dubban Jama'ar dake karkashinka akwai da yawa wadanda suka fika kusanci da kuma daraja awajen Allah. Don haka ka kiyayi kanka!!! Kar ka rika raina mutane ko cin mutuncinsu.
- HAKURI BISA BALA'I: Komai tsananin da kake ciki, kar ka fasa gode ma Allah da yin biyayya agareshi. Kada talauci ko tsananin rayuwa su sanyaka ka munana zatonka ga Allah, ko kuma ka sa'ba dokokinsa. Ka sani cewar Allah yana jarabtar wadanda yafi so ne daga cikin bayinsa. Kuma kowacce musiba tare da sauki kala-kala da zasu biyo bayanta.
- WOFINTA DUNIYA : Hakika ita duniya tsinanniya ce awajen Allah. In banda Malamai da almajirai da zikirin Allah da abinda ke kewaye dashi. Don haka babu wanda duniya tafi wahalarwa sai wanda ya damu da ita.
Wadanda suka dauki duniya ba komai ba, su suka huta. Sune wadanda koda duniyar tazo garesu sai su dauketa su bayar domin guzurin lahirarsu. Kuma basu yin bakin ciki koda duniyar bata zo musu ba.
Ya Allah kasa mu dace da samun yardarka da kusanci gareka. Ya Allah yi salati da tasleemi bisa Annabinka Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da dukkan Sahabbansa da dukkan mutanen kirki har zuwa ranar sakamako.