RAYA DARAREN WATAN RAMADAN DA IBADA



*-RAYA DARAREN WATAN RAMADHANA DA IBADA*

Manzon Allah ﷺ yana cewa:
*(Duk wanda ya raya daren Ramadhana da ibada,yana mai Imani kuma yana mai neman ladar Allah,an gafarta masa abinda ya gabatar na zunubansa)*
@ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ﻭﻣﺴﻠﻢ.

Allah yana baiyana masa bayinsa na musamman sai ya siffantasu da raya dare da yin sallah.

Allah yana cewa:
*(ﻭﻋﺒﺎﺩ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻳﻤﺸﻮﻥ ﻋﻠﻰ ﺍﻷﺭﺽ ﻫﻮﻧﺎً ﻭﺇﺫﺍ ﺧﺎﻃﺒﻬﻢ ﺍﻟﺠﺎﻫﻠﻮﻥ ﻗﺎﻟﻮﺍ ﺳﻼﻣﺎً.ﻭﺍﻟﺬﻳﻦ ﻳﺒﻴﺘﻮﻥ ﻟﺮﺑﻬﻢ ﺳﺠﺪﺍً ﻭﻗﻴﺎﻣﺎ‏)*
@ﺍﻟﻔﺮﻗﺎﻥ 63 ـ 64.

Yin sallar dare ya kasance daga cikin manyan halayen Manzon Allah ﷺ .

Daga A’isha R.A tana cewa:
*”Kada ku daina yin sallar Qiyamul laili domin Manzon Allah ﷺ ya kasance baya barin yin sallar dare,idan baya da Lafiya ko yana cikin nauyin jiki sai yayi sallar Azaune”*

Umar Bin Khaddab R.A ya kasance yana yin sallar cikin dare abinda Allah ya sauwake masa,idan rabin dare yayi sai ya tayar da Iyalinsa suyi sallah,sai ya riqa karanta wannan aya:-
*(ﻭﺃﻣﺮ ﺃﻫﻠﻚ ﺑﺎﻟﺼﻼﺓ ﻭﺍﺻﻄﺒﺮ ﻋﻠﻴﻬﺎ ﻻ ﻧﺴﺄﻟﻚ ﺭﺯﻗﺎ ﻧﺤﻦ ﻧﺮﺯﻗﻚ ﻭﺍﻟﻌﺎﻗﺒﺔ ﻟﻠﺘﻘﻮﻯ)*
@ﻃﻪ ﺍﻵﻳﺔ 132.

Ibn Umar R.A ya kasance yana karanta wannan aya:-
*(ﺃﻣﻦ ﻫﻮ ﻗﺎﻧﺖ ﺁﻧﺎﺀ ﺍﻟﻠﻴﻞ ﺳﺎﺟﺪﺍً ﻭﻗﺎﺋﻤﺎً ﻳﺤﺬﺭ ﺍﻵﺧﺮﺓ ﻭﻳﺮﺟﻮ ﺭﺣﻤﺔ ﺭﺑﻪ)*
@ﺍﻟﺰﻣﺮ ﺍﻵﻳﺔ 9.
Sai yace:
*”Wannan aya tana maganane akan Usman Dan Affan R.A”*

Ibn Hatim yana cewa:
“Ibn Umar R.A yana fadin hakane saboda yawan yin sallar dare na sayyadina Usman R.A,ya kasane yakan sauke alqurani acikin raka’a daya”

Daga Alqamah Bn Qais yana cewa;Na kwana tare da Abdillahi Dan Mas’ud R.A a wani dare,sai ya tashi yake sallah cikin farkon dare,ya kasance yana yin karatu daki daki irin karatun limami acikin masallaci,har sai da dare ya rage kadan sai ya tashi yayi wutiri”

Yana da kyau kuma sunnane ga mai Azumi ya kiyaye sallar Tarawinsa gaba daya tun daga farkon azumi har zuwa karshe,kuma yayi tare da liman a masallaci shine yafi lada.

Saboda fadin Manzon Allah ﷺ:-
*(Dukkan wanda yayi sallar Tarawi ko qiyamul laili tare da liman kuma ya tsaya tare da liman har aka kammala sallar,za’a rubuta masa ladar yayi sallah dukan daren baki daya)*
@ﺭﻭﺍﻩ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﺴﻨﻦ.

Allah ne mafi sani.
Post a Comment (0)