RENON YARO (HADHANAH) DA BAYANIN HUKUNCE-HUKUNCENSA

RENON YARO (HADHANAH) DA BAYANIN HUKUNCE-HUKUNCENSA 

https://chat.whatsapp.com/Cnf26Q8MPqz9yUYU1nxqRq

*TAMBAYA*❓

ASSALAMU.ALAIKUM MALAN MUNA GODIYA DA GUDUMUWAAR DU KUKE BADAWA..... MALAN INADA TAMBAYA KAMAR HAKA MALAN MAYE HUKUNCIN RAINON YARO DA SHAYARWA KUMA WACE AYACE KO HADISI SUKAI MAGANA AKAN HAKA NAGODE ALLAH YASA WANNAN SHINE SILAR SHIGA ALJANNA Ameeen...👏🏻

*AMSA*👇


Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu

 *Menene "Hadhanah (reno)":*
 A harshen larabci "hadhanah" tana nufin tarbiya ma yaro da bashi kula, an ciro kalmar ce daga "hidnu" mai ma'anar: gefe; wannan kuma saboda kasancewar mai reno (ko wakilin yaro) ya kan sanya jariri a gefensa. Shi kuma wanda ake kiransa "haadinu, ko haadinah" shine: Mutumin da aka bashi karamin yaro don ya kula da shi, ya kuma riqa tarairayarsa (renonsa).

A shari'ance kuma "hadhanah" itace: Mutum ya tsayu wajen kula da yaron da bai gama sanin fari-da-baqi ba, ko kuma ba zai iya cin gashin-kansa ba, da yi masa tarbiyya da irin abinda zai gyara masa duniyarsa; ta ɓangaren jikinsa, da kuma ta ɓangaren ma'ana, tare da kare shi daga barin duk abinda zai cutar da shi.

 *Hukuncin "hadhanah":* Hukuncin reno ya kan wajaba akan mai yin hadanar;
matuqar babu wanda zai yi hadanar in banda shi, ko kuma akwai waninsa sai dai kuma yaron da za a yi ma renon ya
qi karbar wani in banda shi; a nan sai
karbarsa ya zama wajibi akansa; wannan kuma saboda idan har bai
karbe shi ba; yaron ka iya halaka, ko kuma alal aqalla zai cutu; don haka dole ne akansa ya tsamar da shi ko ya kiyaye shi. A wani lokaci kuma hadhana ka iya zama wajibin da wani zai iya dauke ma wani (farilla ta kifayah) idan akwai mutanen da za su yi renon, ko a ce yaron zai karbi mutane da-dama.

Wanene haqqin reno ke tabbata masa?
Reno na iya kasancewa ga mata ko ga mazaje matuqar dai sun cancanci yinsa; sai dai kuma ana bada fifiko ga mata akan maza; saboda (mata) sun fi tausayi da sassauta ma yaro. Amma idan matan da ake da su basu da haqqin wannan renon to sai lamarin ya juya zuwa ga mazaje; saboda su kuma mazaje sun fi girman iko wajen kawo abinda zai kare yara, ya kuma tabbatar musu da maslaha.

Renon yaro na kasancewa a hannun iyayensa guda biyu (uwarsa da ubansa);
matuqar akwai aure a tsakaninsu, amma idan basa tare; saboda shikar da ta kasance, to a wannan halin "hadhanar" za ta kasance a hannun uwarsa matuqar bata auri mutumin da bashi da alaqa (ta kusa ko ta nesa) da mijinta na farko ba, wannan kuma saboda faɗinsa (r) ga matar da mijinta ya sake ta, sai kuma ya so ya kwace yaronsa daga gare ta:

" ﺃَﻧْﺖِ ﺃَﺣَﻖُّ ﺑِﻪِ ﻣَﺎ ﻟَﻢْ ﺗَﻨْﻜِﺤِﻲ " ‏
Ma'ana: (ke ce kika fi cancantar ki rene shi matuqar ba ki yi aure ba).

 *Abinda reno ke hukuntawa:*
 Lallai "hadhanah" na hukunta kiyaye yaron da ake renonsa, da riqe shi tare da hana shi zuwa ko aikata duk abinda zai cutar da shi, da yi masa tarbiyya har zuwa girmansa, da aikata duk abinda ke zama maslaharsa; kamar kula da bada abincinsa, da abin shansa, da tsaftace shi; ciki-da-waje, da kula da yin barcinsa da tashinsa, da xauke masa dukkan buqatunsa da abubuwan da ke nema.

 *Sharudan da aka sanya wa mai reno, da abubuwan da suke hana bada "hadhana":* 

Musulunci: Saboda ba a bada kafiri renon ɗan musulmi; domin kuwa Allah ta'alah bai bawa kafirai wata qofa ko kafa da zasu shugabanci musulmai ba, da kuma saboda tsorace ma yaron da ake bashi renon cewa kar ya rudu da kafiri ta vangaren addininsa; har ya iya fitar da shi daga Musulunci i zuwa ga addininsa na kafirci.

Balaga da hankali: Domin yaro qanqani ba a bashi renon yaro, haka shima mutum mahaukaci ko mai tabin hankali; wannan kuma saboda basu da ikon juya lamarin wadanda suke yi musu reno; hasali ma! Su kansu suna
buqatar wanda zai kula da su ya riqa yi musu hadhana.

Mai hadhana dole ya zama amintacce ta
bangaren addini, kuma kamamme: Saboda ba a bada reno ga mutum mai ha'inci, ko
fasiqi; saboda kasancewarsu ba a aminta da su; hasali ma barin yaro a wajensu matsala ce ga yaron (ma'ana: cutuwa ne) a ransa da kuma dukiyarsa.

Dole kuma mai renon ya zama ya kubuta daga cututtuka da suke yaɗuwa daga mutum zuwa mutum, kamar kuturta, da makamancin haka.

Dole mai reno ya zama wanda ya iya jujjuya dukiya: Saboda ba a bada reno ga wawa mai almubazzaranci; tsoron kar ya lalata kuɗi ko dukiyar yaron da yake renonsa.

Dole ne kuma ya zama da ba bawa ba:
Saboda ba a bada reno ga mutumin da bashi da 'yanci (bawa); kasancewar "hadhana" shugabanci ne; bawa kuma bashi da shugabanci akan kowa.

Waɗannan sharudan sun game mazaje da mata da zasu yi aikin reno, amma ita kuma mace ana qara sharadi guda ɗaya akanta; wanda kuma shine: Kar matar ta zama tana auren mutumin da babu wata dangantaka tsakaninsa da wanda take reno; saboda a wannan lokacin zata shagalta da hidima ga mijinta da bashi haqqoqinsa; da kuma saboda faɗinsa (r):
" ﺃَﻧْﺖِ ﺃَﺣَﻖُّ ﺑِﻪِ ﻣَﺎ ﻟَﻢْ ﺗَﻨْﻜِﺤِﻲ " .
Ma'ana: (ke ce kika fi cancantar ki rene shi matuqar baki yi aure ba).
Kuma "hadhana" tana faduwa idan aka samu abu guda daga cikin abubuwan da suke iya hana "hadhanar"
waɗanda suka gabata, ko kuma idan aka rasa sharadi daga cikin sharudanta.

 *Wassu daga cikin hukunce-hukuncen da suke rataya akan renon yara (hadhanah):*

Idan daya daga cikin uwa ko uban yaron da ake renonsa ya yi tafiya, mai tsayi, ba kuma da nufin cutar da wanda ake renonsa ba, hanyar kuma ta zama amintacciya, to a nan uban yaro shine ya fi cancantar ya dauki dawainiyar renonsa; sawa'un shi uban shine matafiyin, ko shine mazaunin gari da gida; saboda kasancewar uba shine alhakin tarbiyyar yaro ke wuyansa, don haka idan da zai zamto a nesa sai dansa ya tozarta.

- Amma idan tafiyar dayansu ta kasance ne zuwa ga wani gari da ke kusa-kusa (wanda nisansa bai kai nisan garin da ake yin sallar qasaru ba) to a nan "hadhanar" za ta zama a wuyan uwar yaro; sawa'un itace mai tafiyar ko ita ce a zaune a gida, saboda uwa tafi tsananin tausayin yaro, kuma uban a irin wannan tafiyar zai iya bincikan halin da yaron ke ciki.

- Amma idan tafiyar ta zama tana da nisa, kuma buqata ce ta hukunta ta, sai kuma hanyar ta zama bata da aminci (ko a-dawo, ko ba-a-dawo ba) to a nan "hadhanar" yaro zata zama a wuyan mutumin dake zaune a gida daga cikinsu.

- "Hadhana" tana qarewa ne lokacin da yaro ya cika shekaru bakwai, daga nan kuma sai a bawa da namiji zabin ya kasance a wurin ubansa ko wajen uwarsa; sai kuma ya ci gaba da zama a wajen wanda ya zaba daga cikinsu; wannan kuma saboda faɗinsa (r):
" ﻳَﺎ ﻏُﻼﻡُ ! ﻫَﺬَﺍ ﺃَﺑُﻮﻙَ ﻭَﻫَﺬِﻩِ ﺃُﻣُّﻚَ؛ ﻓَﺨُﺬْ ﺑِﻴَﺪِ ﺃَﻳِّﻬِﻤَﺎ ﺷِﺌْﺖَ، ﻓَﺄَﺧَﺬَ ﺑِﻴَﺪِ ﺃُﻣِّﻪِ ﻓَﺎﻧْﻄَﻠَﻘَﺖْ ﺑِﻪ " ‏
.
Ma'ana: (Ya kai yaro! Wannan shine ubanka, wannan kuma itace uwarka; don haka sai ka kama hannun duk wanda ka so daga cikinsu. Sai yaro ya kama hannun uwarsa, sai ta tafi da shi). Kuma lallai wannan hukuncin na bada
zabi ga yaro Umar da Aliyu -t- suma sun yi hukunci da irinsa. Ba a bada zabi ma yaro kan mamarsa da babansa har sai idan kowanne daga cikinsu ya cika sharudan hadhana da suka gabata. Abinda yasa kuma aka qayyade bashi wannan zabin da shekaru (7) shine saboda daga wannan shekaran ake fara umurtar yaro da sallah. Kuma idan yaro ya zabi ubansa to zai kasance a wajensa ne dare da yini; domin ya riqa tarbiyyantar da shi, amma kuma baya halatta ya riqa hana shi ziyartar uwarsa mahaifiya. Idan kuma uwarsa ya zaba to a nan zai riqa kasancewa ne a wajenta da daddare, ya kuma ci-gaba da kasancewa a waje ko gidan ubansa da rana; don kula da tarbiyyarsa, kuma saboda lokacin yini lokaci ne na fita biyan buqatu da aikata sana'oi.

Amma ita kuma 'ya mace idan ta kai shekaru bakwai (7) to dole ta kasance a wajen ubanta; saboda shine kawai zai fi kula da ita, kuma shine mutumin da ya fi haqqin zama waliyyinta (kula da lamarinta har ta kai lokacin aure), kuma saboda tana kusantar shekarun aure; shi kuma uba shine waliyyinta da za a nemi aurenta a wajensa, kamar yadda kuma shine ya fi sanin mutumin da zai dace da ita daga cikin mutanen da za su zo neman aurenta. Sai dai kuma don an ce 'ya mace ta kasance a wajen ubanta ba za a hana uwarta ziyartat ta ba idan har ta so hakan; sai dai in akwai abinda ake tsorace mata; na bacin tarbiyya, ko wanin haka, to a nan kam ya halatta a hana wannan. Amma idan uban ba zai iya kula da ita ba; ko don saboda aiyukansa, ko don tsufa, ko rashin lafiya, ko kuma
qarancin addininsa, Sai kuma uwar ta zama ita tafi uban dacewar ta dukkan fiskoki to a nan uwa ita ce ta fi uban cancantar riqe ta. Haka kuma lamarin yake; idan uban ya auri wata mata, ya kuma ajiye 'yar tasa a gaban sabuwar matat tasa; sai ba a yi sa'a ba; ta yadda ta zama tana cutar da ita; ta fiskar zaftare mata wassu haqqoqinta to a nan ma uwar yarinyar ta haqiqa itace tafi cancantar ta yi mata hadhana.

- Kuɗin biyan me reno (hadhana) –sawa'un mai yin hadanar uwa ce ko watanta- za a fitar da shi daga dukiyar wanda ake renonsa; matuqar dai yana da kuɗi. Ko kuma daga kuɗin waliyyin yaron da duk wanda ciyar da yaron ke kansa; matuqar yaron bashi da dukiya.

([1]) Bukhariy ya ruwaito shi (lamba: 2646), da Muslim (lamba: 1444).
([2]) Bukhariy ya ruwaito shi (lamba: 5100), da Muslim (lamba: 1447), lafazin muslim ne.
([3]) Bukhariy ya ruwaito shi (lamba: 5100), da Muslim (lamba: 1447).
([4]) Muslim ya ruwaito shi (lamba: 1452).
([5]) Bukhariy ya ruwaito shi (lamba: 5099), da Muslim (lamba: 1444).
([6]) Bukhariy ya ruwaito shi (lamba: 2660).
([7]) Ahmad ya ruwaito shi (2/182), da Abu-dawud (lamba: 2276), da Alhakim (2/207), ya kuma inganta shi, Az-zahabiy ya wafaqa masa, Shi kuma Albaniy yace hadisi ne hasan (Irwa'ul galil, lamba: 2187).
([8]) Shi ne hadisin da ya gabata..
([9]) Ahmad ya ruwaito shi (2/246), da Abu-dawud (lamba: 2277), da At-tirmiziy (lamba: 1375), ya ce: hadisi ne hasan ingantacce, da Alhaakim (4/97), ya inganta shi, Az-zahabiy kuma ya wafaqa masa, Albaniy ma ya inganta shi (Irwa'ul galil, lamba: 2192).

‎Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
 *_Group Admin: ▽_*
 *MAL. HAMISU IBN YUSUF*

Post a Comment (0)